Hatsarin Babbar Mota da Bas Ya Lakume Rayukan Mutum 5 a Anambra
- Wani mummunan hatsari ya yi ajalin fasinjojin motar bas mata 5 a jihar Anambra, wasu da dama sun ji raunuka
- Ganau sun bayyana cewa kwantenar da wata babbar mota ta ɗauko ce ta faɗa kan Bas ɗin, ta murkushe mutanen a babban titin Awka
- Hukumar kiyaye haɗurra (FRSC) ta bayyana cewa tuni jami'ai suka ɗauke gawarwakin kuma suka kai majinyatan asibiti
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Anambra - Wani mummunan hatsari ya rutsa da motar bas ta haya kirar L300 da kuma babbar motar dakon kaya 'Leyland' a mahadar Odumudu da ke kan babban titin Nteje-Awka, jihar Anambra.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa hatsarin ya lakume rayukan fasinjoji biyar yayin da wasu biyar kuma suka samu raunuka daban-daban.
Hadarin wanda ya auƙu da misalin karfe 7:30 na safiyar ranar Juma’a ya rutsa da mutane 10, maza uku da mata bakwai.
Yadda hatsarin ya auku
A cewar wani ganau da abun ya faru a gabansa, lalacewar wani ɓangare na titin ne ya haddasa hatsarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutanen da ke wurin sun ce motocin biyu sun taho ne daga bangarori daban-daban, amma da suka isa wuri mara kyau a titin, sai kwantenan da ke makale da babar motar ta faɗa kan bas din tare da murkushe wasu daga cikin fasinjoji.
Da take tabbatarwa, muƙaddashin kakakin hukumar kiyaye haɗurra ta Anambara (FRSC), RC Margaret Onabe, ta ce mutum biyar suka mutu yayin da wasu biyar suka ji raunuka.
A cewarta, jami'an sashin ceto na hukumar FRSC daga RS5.33 da ke Nteje sun kai waɗanda suka jikkata zuwa asibitin Divine Care, Umunya domin kula da lafiyarsu.
Haka zalika sun ɗauki gawarwakin waɗanda Allah ya yi wa rasuwa zuwa Asibitin Chira domin kwararrun likitoci su tabbatar da mutuwarsu kafin daga bisani su kai su ɗakin aje gawa na Nteje.
A halin yanzu da muke kawo muku wannan rahoto, Kwamandan sashin ceto tare da hadin gwiwar Kwamandan Nteje, na kokarin kawar da cikas din da hadarin ya haifar.
Duka waɗanda suka mutu mata ne - FRSC
Shugaban FRSC na jihar Anambra, Adeoye Irelewuyi, ya jajantawa iyalan mamatan. Ya kuma yi fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.
The Nation ta rahoto Shugaban FRSC na cewa:
"Mutane 10 da suka hada da maza 3 da mata 7 ne hatsarin ya rutsa da su, mata biyar daga ciki suka rasa rayukansu."
Adeoye ya bukaci masu ababen hawa da su yi tuki cikin taka tsantsan, kuma su kula da yanayin tituna yayin da suke tafiya.
Innalillahi, Bene Mai Hawa 20 Ya Rushe Kan Jama'a a Babban Birnin Jihar PDP
A wani rahoton na daban Mutane da dama sun samu raunuka yayin da wani gini mai hawa 20 ya kife a Asaba jihar Delta da yammacin Alhamis.
'Yan Bindiga Sun Kuma Kai Mummunan Farmaki Da Tsakar Dare, Sun Yi Ajalin Mutane 11, 'Yan Sanda Sun Yi Martani
Ginin otal ɗin na biliyoyin Naira da ke daura da Delta Mall ya ruguje ne da yammacin ranar Alhamis yayin da ma'aikata ke tsaka da aiki.
Asali: Legit.ng