Matasa Sun Rushe Gidan Malamin Da Ke Halatta Cin Naman Kare A Kaduna

Matasa Sun Rushe Gidan Malamin Da Ke Halatta Cin Naman Kare A Kaduna

  • Wasu matasa sun rushe gida da kuma makarantar wani malami da ya ke ikirarin halatta cin naman kare
  • Lamarin ya faru ne a Unguwar Nassarawa da ke jihar Kaduna inda matasan su ka ce ya sabawa koyarwar Musulunci
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, ASP Mansir Hassan ya ce ko da akwai 'yancin addini ba za su bari a jawo rigima a jihar ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Wasu fusatattun matasa sun rushe gidan wani malami da ke ikirarin halaccin cin naman kare.

Matasan sun kuma rusa makarantar malamin wanda su ka ci naman kare da dalibansa a Unguwar Nassarawa da ke jihar Kaduna.

Matasa sun rusa gidan malamin da ke cin naman kare a Kaduna
Matasa Sun Dauki Mataki Kan Malamin Da Ya Halasta Cin Naman Kare. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Meye ya jawo rusa gidan malamin a Kaduna?

A ranar Talata ne 12 ga watan Satumba matasan su ka yi zanga-zanga tare da rushe gidan malamin.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Gida Gida Ya Ce Auren Zaurawa Na Daga Cikin Tallafin Rage Radadin Wahala, Ya Ware Makudan Kudade

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahotanni sun tabbatar da cewa wanda ake zargin ya yanka karen tare da tserewa bayan ya fahimci ana nemanshi.

Hukumar 'yan sanda a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Mansir Hassan, cewar Trust Radio.

Hassan ya ce yanzu haka rundunarsu na kan binciken lamarin inda ya tabbatar cewa malamin ya ce bai yanka karen don suna a gidansa ba.

Makamin ya tabbatar da cewa addininsu ya yarda da haka kuma a cewarsa ba su saba wa addinin da suke bi ba.

Meye mabiyan malamin ke cewa a Kaduna?

Daya daga cikin mabiya akidar halatta cin naman kare a unguwar da bai ambaci sunansa ba ya ce su fa Musulmai ne kuma sun yarda da Alkur'ani.

Ya ce:

“Mu fa Musulmai ne da muka yarda da littafin Al’kurani a matsayin littafin ibada, kuma da littafin muke ibada, ibadanmu ya sha bamban da na sauran mutane.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Addini Da Wasu Mutum 3 a Wata Jihar Arewa

“Kuma Najariya kasa ce da ta bai wa kowa ’yancin yin addininsa kuma a iya fahimtarmu, babu inda Allah ya hana a ci kare.
“Sai muka ce duk wanda ya ce an saba mishi ko an saba wa Allah, toh ya kawo mana ayar, idan muka gani muka fahimta sai mu roki Allah gafara mu daina.”

Kakakin rundunar ’yan sanda a jihar ya ce ko da Najeriya ta ba da 'yancin yin addini amma ba za su bari wasu su jawo rigima ba.

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Wurin Ibada a Kaduna

A wani labarin, wasu miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki kan Cocin St. Raphael Parish da ke garin Fadan Kamantan yankin Kafanchan a kudancin jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce yayin harin na daren Alhamis, 'yan bindigan sun kone daya daga ciki gidajen Cocin tare da wani mai shirin zama Malamin Coci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.