Ana Binciken Mutanen da ke da Alaka da Emefiele a Badakalar Naira Tiriliyan 7

Ana Binciken Mutanen da ke da Alaka da Emefiele a Badakalar Naira Tiriliyan 7

  • Lambar mutanen Godwin Emefiele ta fito a binciken da ake yi domin bin diddikin bankin CBN
  • Bola Ahmed Tinubu ya dauko hayar tsohon shugaban FRC, Jim Obazee, ya ba shi wannan aiki
  • Kwamitin da aka kafa ya fara kokarin cafke na kusa da tsohon Gwamnan CBN a binciken da ake yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Watakila nan da ‘yan kwanaki kadan mutanen Najeriya su ji labarin badakalar da za ta shiga cikin mafi girma a tarihin kasar.

Wani rahoton The Guardian ya bayyana cewa kwamitin bincike na musamman da aka kafa domin ayyukan bankin CBN ya tono babban aiki.

Wannan kwamiti ya kama hanyar bankado wasu da ake zargi su na da hannu a satar makudan kudin da adadinsu zai iya kai Naira tiriliyan 7.

Mr. Godwin Emefiele
Tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Binciken mutanen Godwin Emefiele

Kara karanta wannan

Shari’ar zabe, 50% da Hanyoyi 3 da Za a Iya Bi Wajen Gyara Zabe – Ministan Jonathan

Godwin Emefiele ya jagoranci bankin na tsawon shekaru tara, tun bayan da Goodluck Jonathan ya tsige Sanusi Lamido Sanusi a tsakiyar 2014.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton da aka samu ya ce yanzu haka ana duba takardu, bayanai da kalaman da aka samu a bankin, kuma za a iya cafko wasu mutanen dabam.

Duk da ba a tabbatar da gaskiyar zancen ba, ana cewa kwamitin Obazee zai binciki wasu jakadun Najeriya da ke kasar Larabawa a kan zargin.

Wasu manya da ke kasashen ketare sun yi kokarin ba abubuwan da su ka faru a CBN daurin gindi, yanzu haka bincike ya fara fallasa abubuwa.

CBN: Za a iya cafko manyan mutane

Alamu na nuna za a shiga bankunan kasashen ketare domin fadada binciken badakalar satar da ake zargin an tafka ta karkashin CBN.

Zuwa yanzu wasu na kusa da shugaban kasa sun fara kokarin takaita binciken da za a gudanar, sai dai Obazee bai sauraron kowa sai Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kitimurmura Yayin Da Gwamnan PDP Ya Sallami Dukkan Hadiman Mataimakinsa, An Bayyana Dalili

An fara ambato sunayen fitattun ‘yan siyasa da manyan ‘yan kasuwa a badakalar canjin kudi da sare-tsaren tallafi da bankin CBN ya kawo.

Ta haka aka bankado zargin badakalar Naira tiriliyan 7 da Emefiele da mutanensa za su yi bayani, yanzu haka kwamitin ya na tsakiyar aikinsa.

Baya ga CBN, an ji yadda binciken ya ke shafar sauran manyan hukumomin tarayya.

Tinubu ya dauko Jim Obazee

Kun ji cewa Jim Obazee ya na da hurumin binciken abubuwan da su ka faru a CBN – bankin da ke alhakin kula da duk harkokin kudi a doka.

Idan kwamitin ya kammala aikinsa, za a san gaskiyar duk abubuwan da su ka faru a lokacin da Godwin Emefiele yake rike da bankin CBN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng