Gamayyar Kungiyar Magoya Bayan APC Na Son Tinubu Ya Nada Shugabanta Minista Daga Kaduna

Gamayyar Kungiyar Magoya Bayan APC Na Son Tinubu Ya Nada Shugabanta Minista Daga Kaduna

  • Gamayyyar ƙungiyoyin magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa sun hango wanda ya fi dacewa ya zama minista daga Kaduna
  • Ƙungiyar ta shawarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugabanta, Alhaji Kailani Muhammed, minista daga jihar Kaduna
  • Ƙungiyar ta bayyana hakan ne dai ta hannun darektan watsa labaranta, wanda ya lissafo dalilian da yakamata su sanya a ba Kailani kujerar minista

FCT, Abuja - Gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Darekta Janar ɗinta, Alhaji Kailani Muhammed, a matsayin minista daga jihar Kaduna.

Ƙungiyar ta yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa ta hannun darektan watsai da hulɗa jama'a ɓa ƙungiyar, Dr. Saleh Bin-Ahmed, a birnin tarayya Abuja, ranar Talata, 12 ga watan Satumba, cewar rahoton NAN.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Mambobin Kungiyar NURTW Suka Ba Hammata Iska a Abuja, Bayanai Sun Fito

An shawarci Tinubu kan ministan Kaduna
Kungiyar na son a saka musu kan wahalar da suka yi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban ƙasa Tinubu dai ya zaɓi tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin minista daga Kaduna, amma majalisar dattawa ta ƙi amincewa da shi bisa rahoton tsaron da aka gabatar a kansa.

Dalilan ƙungiyar na neman a naɗa Kailani minista

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan jam'iyyar APC na ƙasa na kira ga shugaban ƙasan mu Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin ministan Kaduna da shugaban ƙungiyar, Injiniya Kailani Muhammed."
"Wannan shi ne dalilan da zai sanya APC ta sake komawa mulki cikin sauƙi a shekarar 2027, bisa cewa an biya ƙungiyoyin goyon baya wahalar da suka sha kuma an dama da su a gwamnati."

A cewar Bin-Ahmed, Kailani haziƙin ɗan siyasa ne mai taimakon jama'a wanda ya ƙware a aikin gwamnati, gogaggen ɗan jarida, mai sharhi kan al'amuran jama'a, sannan uwa uba kuma mai samar da sabbin ra'ayoyi.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Hadimar Buhari Ta Kai Karar Peter Obi Wajen DSS, Ta Bayyana Kwararan Dalilanta

“Yana da abin da ake buƙata domin samar da romon dimokuraɗiyya ga ƴan Najeriya." A cewarsa.
"Muna fatan cewa Shugaba Tinubu zai yi duba da idon basira kan kiraye-kirayen da al'umma ke yi, domin babu wani lokaci wanda ya wuce na yanzu."

Fadar Shugaban Kasa Ta Magantu Kan Ministoci

A baya rahoto ya zo cewa fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu zai tsaya tsayin daka domin tabbatar da cewa ministoci sun yi aikin da ya dace.

Mai magana da yawun shugaban ƙasan, Ajuri Ngelale, shi ne ya bayyana hakan inda ya ce Shugaba Tinubu ba zai lamunci lalaci daga ministocinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng