Tinubu Zai Tabbatar Da Ministocinsa Sun Yi Abinda Ya Kamata, Fadar Shugaban Kasa

Tinubu Zai Tabbatar Da Ministocinsa Sun Yi Abinda Ya Kamata, Fadar Shugaban Kasa

  • Shugaba Tinubu ya ce zai sanya idanu sosai wajen ganin ministocinsa sun yi aiki yadda ya kamata
  • Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Cif Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a yayin hira da 'yan jarida
  • Ya bayyana cewa Tinubu ba zai lamunci lalaci daga ministocinsa ba, zai bi su ƙafa da ƙafa don tabbatar da sun yi aiki

FCT, Abuja - Mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu Cif Ajuri Ngelale, ya ce shugaban zai tabbatar da cewa ministocinsa sun yi aiki yadda ya kamata.

Ya bayyana hakan ne a yayin da ake zantawa da shi a gidan talabijin na Channels kan sabbin ministocin da aka naɗa.

Tinubu ya ce zai tabbatar ministocinsa sun yi abinda ya dace
Tinubu ba zai lamunci lalaci daga ministocinsa ba. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ba zai lamunci lalaci ba, zai tabbatar an yi abinda ya kamata

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Hango Wani Sabon Abu Da Zai Faru a Mulkin Shugaba Tinubu

Ngelale ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ba zai lamunci lalaci daga ministocinsa ba, inda ya ce shugaban zai bisu ƙafa da ƙafa don tabbatar da cewa sun yi ayyukansu yadda ya dace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma ce Tinubu ya yi ƙoƙarin zaɓo mutanen da suka dace ne ta hanyar lura da ilimin da suke da shi da kuma gogewar da suke da ita a ayyukansu na baya kamar yadda The Eagle Online ta wallafa.

Ngelale ya kuma ƙara da cewa idan 'yan Najeriya suka yi dubi na tsanaki, za su ga cewa duk mutanen da Bola Tinubu ya naɗa a matsayin ministoci, sun dace da inda aka tura su.

Ministocin Tinubu za su laƙume biliyan 8.6

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan maƙudan kuɗaɗen da aka ƙididdige cewa ministocin Shugaba Bola Tinubu za su laƙume a cikin shekaru huɗu masu zuwa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Aike Da Sabon Gargadi Ga Wike Da Sauran Ministocinsa

Ƙididdigar ta nuna cewa ministocin na Tinubu za su laƙume kuɗaɗen da yawansu ya kai naira biliyan 8.6 a wajen biyan albashinsu da alawus da za a riƙa ba su cikin shekaru huɗu masu zuwa.

Ana kuma hasashen cewa kuɗaɗen za su iya ƙaruwar da zarar an tabbatar da sabon ƙarin albashin da ake shirin yi wa ma'aikatan gwamnatin ƙasar.

Tinubu ya bai wa ministocinsa sabon umarni

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan umarnin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa ministocinsa na su fara aiki ba tare da ɓata lokaci ba.

Shugaban ya kuma buƙaci sabbin ministocin da su fifita ra'ayi da jin daɗin 'yan Najeriya fiye da wata jiha ko wani yanki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel