Lokacin da Aka Yi Alkawari Ya Wuce, Matatar Dangote Ba Ta Fara Aiki Ba a Najeriya

Lokacin da Aka Yi Alkawari Ya Wuce, Matatar Dangote Ba Ta Fara Aiki Ba a Najeriya

  • An yi alkawarin Najeriya za ta fara tace mai a cikin gida ba tare da an dogara da kasashen waje ba
  • Kwanakin baya Muhammadu Buhari ya shaida haka da ya ke kaddamar da matatar Dangote
  • Har zuwa yau, kusan 100% na man da ake amfani da shi a kasar nan daga matatun waje yake zuwa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Matatar kamfanin Dangote da ya kamata ta rika tace gangunan danyen mai 650, 00 a kowace ba ta soma aiki ba tukuna.

A wani rahoto da aka samu daga Punch a ranar Talata, an fahimci cewa alkawarin da aka yi na fara tace mai a gida bai tabbata ba.

Mai girma Muhammadu Buhari ya kaddamar da matatar a watan Mayu, ya kuma yi alkawarin cewa zuwa gusta za a fara tace mai.

Kara karanta wannan

Hatsarin Kwale-Kwale: Yadda Mutum 16 Yan Gida Daya Suka Mutu a Jihar Arewa

Dangote
Bikin kaddamar da matatar Dangote Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Za a ga man Dangote daga Yuli ko Agusta

Tsohon shugaban kasar ya shaidawa duniya ana sa ran fara ganin man da matatar ta tace a kasuwa daga karshen Yuli ko farkon Agusta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya ce zuwa yanzu ko digon tatattacen mai bai shogo kasuwa ba, har gobe kamfanin NNPC ne yake shigo da mai daga kasar waje.

NNPC ke kawo man fetur daga ketare

A watan Yuni, mai magana da yawun bakin NNPC, Garba Deen Muhammad yace za su rage shigo da mai da zarar matatar nan ta fara aiki.

Wasu majiyoyi daga kungiyar manyan dillalan mai a Najeriya (MOMAN) sun tabbatar da cewa abin da NNPC ke shigo da shi ya ragu.

Shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed, ya tabatar da haka da yake magana da ‘yan jarida.

Dangote ya dauko namijin aiki - Farfesa

Kara karanta wannan

Yadda Binciken Da Tinubu Yake Yi Zai Tona Barnar da Buhari Ya Yi – Kanal Dangiwa

Da mu ka zanta da wani Farfesan jami’a a fannin ilmin injiniyanci, ya fada mana gaskiya za a dauki lokacin kafin matatar ta tace mai.

Masanin ya shaidawa Legit cewa Aliko Dangote ya dauko katafaren aiki mai girma da duk duniya babu kasar da ta gina irin matatarsa.

Daga cikin matsalolin da matatar za ta fuskanta akwai samun isasshen wutan da za su tada na’urorin da za su yi wannan aiki a Legas.

Da aka nemi jin ta bakin ma’aikatan kamfanin da ke Lekki, ba su yarda sun ce uffan a kan batun matatar man da ta ci sama da $19bn ba.

Aliko Dangote da Muhammau Buhari

An taba rahoto Alhaji Aliko Dangote ya na yabawa Muhammadu Buhari da gwamnatocin jihar Legos da aka yi daga 1999 zuwa yau.

Dangote ya ce saura kadan ya fasa ginin matatar, amma Muhammadu Buhari ya kara masa kwarin gwiwa har aka kai ga hango nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng