Gwamnatin Tinubu Tayi Karin Haske a Kan ‘Shirye-Shiryen’ Kirkiro Wasu Haraji
- Gwamnatin tarayya ta tabbatar da ba za a karo dokokin haraji da nufin samun kudin shiga ba
- Bola Tinubu ya jaddada cewa bai da niyyar karawa al’umma haraji a kan wanda su ke biya a yau
- A maimakon haka, sanarwa ta fito daga fadar shugaban kasa a kan rage adadin masu biyan haraji
Abuja - Gwamnatin Najeriya ta bude baki ta yi magana game da abin da wasu su ke tunani na fito da wasu sababbin haraji.
A wata sanarwa da aka samu daga fadar shugaban kasa a karshen makon jiya, gwamnatin tarayya ta fayyace yadda abin yake.
Sanarwar da ta fito a daren yau ta ce gwamnatin Bola Tinubu ba za ta rika tatse jarin ‘yan kasuwa da sunan karbar haraji ba.
Kamar yadda ya yi alkawarin tun kafin ya dare kan mulki, shugaban Najeriyan zai yi kokari ya kawo sa’ida ga marasa karfi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin da aka samu daga fadar shugaban kasa ya kara da cewa akwai yunkurin da ake yi na rage canza dokokin tattalin arziki.
Sanarwar fadar shugaban kasa
"Shin ‘Yan Najeriya su shiryawa karin haraji da yawaitar canjin dokokin biyan haraji?
Ba mu da niyyar kirkiro wasu haraji ko a kakaba sabon tsarin haraji, aikinmu shi ne rage adadin masu biyan haraji
Yayin da za mu daidaita hanyar karbar kudin shiga domin ragewa mutane da kasuwanci nauyin da yake kansu.
Manufar ita ce kaucewa lafta haraji a kan uwar kudi, jari, dukiyar samar da kaya ko kuwa talauci.
Mu na shirin sake duba tare da fito da manyan dokokin shari’a yadda zai takaita yawan bukatar canje-canje a dokar kudi.
- Bola Tinubu
Yanzu haka akwai kwamitin shugaban kasa a karkashin jagorancin Taiwo Oyedele da ke aiki domin gyara tsarin haraji.
G20: Tinubu da Biden a Indiya
Rahoto ya zo cewa Joe Biden ya yi maraba da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu wajen kawo sauyi a bangaren tattalin arziki a Najeriya.
Sannan Shugaban Amurkan ya godewa Tinubu na jajirtaccen shugabancin da ya nuna a kungiyar ECOWAS da su ka hadu a taron G20.
Asali: Legit.ng