Kaduna: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Karar da Ta Kalubalanci Nasarar Sanatan PDP
- Kotun sauraron kararrakin zaben yan majalisa a jihar Kaduna ta tabbatar da nasarar Lawal Usaman na jam’iyyar PDP
- Kotun ta yi fatali da karar da abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC ya shigar yana kalubalantar nasararsa
- Kotun zaben ta sake ayyana Usman a matsayin zababben sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kaduna - Kotun sauraron kararrakin zaben yan majalisar tarayya a Kaduna, ta tabbatar da zaben Lawal Usman na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya.
Dan takarar jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Muhammad Abdullahi, ya shigar da kara kotu inda yake kalubalantar zaben sanatan na PDP kan dalilai hudu.
Abdullahi ya nuna shakku kan sahihancin takardar karatun Usman sannan ya yi ikirarin cewa an samu zartawar kuri'u a lokacin zaben.
Ya kuma yi ikirarin cewa ba a zabi dan takarar na PDP bisa doka ba sannan cewa jam'iyyarsa ta PDP bata dauki nauyinsa ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kotu ta yi watsi da karar dan takarar APC
Sai dai kwamitin kotun zaben mai mutane uku karkashin jagorancin H. Kereng ya yanke hukuncin cewa duk dalilan da mai karar ya gabatar basu da inganci, saboda haka aka yi watsi da su, rahoton The Sun.
Mista Kereng ya ce masu karar sun gaza tabbatar da cewar an kirkiri sakamakon jarrabawar NECO da sauran takardun wanda ake karar ne.
Ya kara da cewar masu karar sun gaza tabbatar da cewar ba a zabi wanda ake kara na farko da kuri'u mafi rinjaye a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu ba.
"Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 182,035 yayin da PDP ta samu 225,066 inda aka samu tazarar kuri'u 43,031. Masu karar sun gaza tabbatar da cewa wanda ake karar bai samu mafi rinjayen kuri'u ba.
"Saboda haka, wannan batun nasara na bangaren wanda ake kara ba mai kara ba," inji shi.
Dangane da batun rashin bin doka, alkalin ya kuma bayyana cewa mai karar ya gaza tabbatar da cewar ba a bi doka ba wajen zabar Mista Usman a matsayin dan takarar PDP ba.
Kotu ta tabbatar da nasarar Usman a matsayin sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya
Ya kara da cewar batun daukar nauyi da zabar yan takara ya rataya ne a wuyan jam'iyyar siyasa ba kotu ba.
"Saboda haka an tabbatar da zabe da dawowar wanda ake kara na farko. Don haka an kori wannan kara," inji shi.
Da yake magana da manema labarai bayan yanke hukuncin, hadimin sanatan, Jalal Falal ya yabawa kotun.
Falal ya ce:
"Kotun ta yi adalci da gaskiya. Mun ci zaben da gaske. Ina kira gare su da su hada kai da Sanatan domin ciyar da jihar gaba."
Wani na hannun damar dan takarar na jam’iyyar APC ya shaidawa jaridar Premium Times cewa mai karar zai sake duba hukuncin kuma za su bayyana matsayinsu nan gaba kadan.
Kotun zabe ta sake tsige wani dan majalisar tarayya na LP, ta maye gurbinsa da wani
A wani labarin, kotun sauraron kararrakin zabe yan majalisun tarayya da ke zama a Enugu ta tsige Chijioke Okereke na jam'iyyar Labour Party (LP).
Har zuwa lokacin da aka tsige shi a ranar Juma'a, 8 ga watan Satumba, Okereke ne dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Aninri/Awgu/Oji-River.
Asali: Legit.ng