DSS Ta Cafke Mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Aisha Ahmad

DSS Ta Cafke Mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Aisha Ahmad

  • Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta cafke mataimakiyar gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Aisha Ahmad
  • Hukumar ta cafke mataimakiyar gwamnan na CBN ne kan zargin samun hannun jari a bankunan Polari, Union/Titan
  • Aisha Ahmad ta bi sahun jerin mataimakan gwamnan CBN da suka tsinci kansu a komar DSS tun bayan da aka dakatar tare da cafke Godwin Emefiele

FCT, Abuja - Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta cafke tare ta tsare mataimakiyar gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Aisha Ahmad.

Aisha Ahmad mataimakiyar gwamnan CBN ce mai kula da daidaito a tsarin a kuɗi.

DSS ta cafke Aisha Ahmad
DSS Ta Cafke Mataimakiyar Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Aisha Ahmad Hoto: NTA
Asali: Twitter

A cewar rahoton PM News, hukumar DSS ta cafke Aisha ne bisa zargin samun hannun jari a bankunan Polaris, Titan/Union ta hanyar da ba ta dace ba.

Kara karanta wannan

“Aikin Mijinta Ne”: Hotunan Yadda Ayarin Motocin Matar Gwamnan Bauchi Suka Makale a Tabo

Wane zargi ake yi wa Aisha Ahmad?

Mataimakiyar gwamnan dai na amsa tambayoyi kan yadda bankin Titan ya samo $300m domin kammala siyan bankin Union.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An naɗa Aisha Ahmad a matsayin mataimakiyar gwamnan CBN a ranar 6 ga watan Oktoban 2017, inda ta maye gurbin Sarah Alade wacce ta yi ritaya a 2017. Majalisar dattawa ta amince da naɗinta a ranar 22 ga watan Maris 2018.

A watan Disamban 2022, an zargi Aisha da taimakawa wajen siyar da bankin Polaris akan farashi mai rahusa domin a duba yiwuwar ba ta muƙamin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Bankin CBN ya musanta zargin inda ya tabbatar da cewa siyar da bankin Polaris an gudanar da shi ne a ƙarƙashin sa idon manyan wakilai na AMCON da CBN.

DSS ta cafke Kingsley Obiora

Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), ta titsiye mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) mai kula da tsare-tsaren tattalin arziƙi, Kingsley Obiora.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ministan Tinubu Ya Tsoma Baki a Rigimar Jam'iyyar APC Da Korar Jiga-Jigai 84

Tambayoyin da aka yi wa Obiora na daga cikin binciken da ake yi ne kan zargin badaƙalar kuɗaɗe da ake yi a ƙarƙashin dakataccen gwamnan CBN, Godwin Emefiele, wanda ya ke tsare a hannun hukumar DSS.

DSS Ta Cafke Shugaban Karamar Hukuma

A wani labarin na daban, Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta tsare dakataccen shugaban karamar hukumar Ijebu ta gabas, Wale Adedayo, kan zargin da ya yi wa Gwamna Dapo Abiodun da badakalar kudade.

Jami'an hukumar DSS reshen jihar Ogun ne suka tsare Adedayo a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumba

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng