Yan Najeriya Sun Yi Zanga-Zanga Saboda Zabtare Kudaden Mutane Da Bankuna Ke Yi

Yan Najeriya Sun Yi Zanga-Zanga Saboda Zabtare Kudaden Mutane Da Bankuna Ke Yi

  • Yan Najeriya sun fito tituna a wasu yankunan Lagas domin yin zanga-zanga a kan yawan cajin da bankuna ne yi
  • Wani bidiyo da aka wallafa a Instagram ya nuna masu zanga-zanga rike da kwalaye dauke da rubutu iri-iri da ke nuna gajiyawarsu kan cajin
  • Wasu masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani ga zanga-zangar, suna masu bayyana cewa irin haka ya faru da su

Yan Najeriya sun gudanar da zanga-zanga a wasu yankuna na jihar Lagas saboda yawan cajin kudade da bankunan kasar ke yi wa jama'a.

Kamar yadda wani bidiyo da @mufasatundeednut ya wallafa a shafinsa na Instagram ya nuna, an yi zanga-zangar ne a Yaba da VI.

Yan Najeriya sun yi zanga-zanga
Yan Najeriya Sun Yi Zanga-Zanga Saboda Zabtare Kudaden Mutane Da Bankuna Ke Yi Hoto: @mufasatundeednut
Asali: Instagram

Yan Najeriya da suka nuna damuwa kan yawan cajin da bankuna ke yi a yan baya-bayan nan sune suka jagoranci zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Zabe: A Karshe Peter Obi Ya Aika Gagarumin Sako Ga Mabiyansa

A wallafar da ya biyo bayan bidiyon, Tunde Ednut ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yana faruwa a karshe! Bankunan Najeriya ba za su so wannan ba! Zanga-zangar da ke gudana a Yaba da VI kan cajin bankuna..Kada na kira kowani banki tukuna!"

Kwastamomi sun nuna fushi a bankuna daban-daban

A cikin bidiyon, masu zanga-zangar sun nuna fushinsu da yawan cajin da bankunan Najeriya ke yi.

Takardun na dauke da rubutu kamar; "Muna son a fayyace mana gaskiya game da kudinmu," "ku daina cire mana kudi haka kawai," kuma "ku ce baku yarda da cajin banki mai yawa ba" da dai sauransu.

Kalli bidiyon a kasa:

Yan Najeriya sun yi martani

Wasu yan Najeriya da suka yi martani ga bidiyon a soshiyal midiya sun bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin.

rikkies_chops_n_meals ta bayyana cewa:

"Mai karamin kasuwanci ba zai ma iya samun bashin banki ba. Wadanda za su baku bashi, kudin ruwa ba sa'anku bane. Kasar shirme gaba daya."

Kara karanta wannan

“Na Ga Rayuwa Da Ciki”: Bidiyon Sauyawar Wata Mata Kafin Ta Haihu Ya Girgiza Intanet

officialdayo_ ya ce:

"A karshe. Dukkan bankuna na kan wannan teburin."

veeglamour.ng ta ce:

"Bayan mun gama wannan muna bukatar kariya a kan yawan data da muke sha muma."

Nelsontycoonn ya ce:

"Zenith da Access kenan. Wadannan mutanen na wasa da kudadenmu."

Legit.ng ta nemi jin ta bakin wasu yan Najeriya kan wannan batu.

Wani dan kasuwa mai suna Mallam Sa'idu ya ce abun ya ishe shi ta yadda ya kan ji kamar ya daina kai kudinsa banki.

Malam Saidu ya ce:

"Gaskiya ya kamata a duba wannan abu domin wasu lokutan ya kan zarta tunanin mutum. Sai ka wayi gari ka ga caji da baka san daga ina suke ba, Sau da dama na kan ji kamar na daina kai ajiyar kudadena banki amma ya mutum ya iya, idan ka ajiye a gida baka tsira ba, a banki kuma ayi ta yi maka dauki daidai kai da guminka."

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Yadda Al’umma Ke Cin Dusa Saboda Yunwa a Wata Jihar Arewa

Yar Najeriya ta mutu a hanyar zuwa Landan

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta gamu da ajalinta. Matashiyar matar ta mutu ne a cikin jirgin sama na Egypt Air a hanyarta ta zuwa birnin Landan, kasar Birtaniya.

An rahoto cewa matashiyar wacce ba a bayyana sunayenta ba, ta baro Najeriya zuwa Landan a cikin jirgin Egpyt Air mai lamba MS 876 zuwa Alkahira a ranar Litinin, 4 ga watan Satumba, ta filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagas lokacin da ta mutu a cikin jirgin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng