Mahaifiya Ta Kona Danta Da Ruwan Zafi Kan Zargin Yawan Neman Mata a Jihar Kuros Riba

Mahaifiya Ta Kona Danta Da Ruwan Zafi Kan Zargin Yawan Neman Mata a Jihar Kuros Riba

  • Wata fusatacciyar mahaifya ta watsawa dan cikinta tafasasshen ruwan zafi kan zargin neman mata a jihar Kuros Riba
  • Matar mai suna Maryam Zakari wacce aka fi sani da Asabe ta aikata hakan ne kan zargin dan nata ya bar ba ta kudi kamar da
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, SP Irene Ugbo ya ce har yanzu ba su da labarin faruwar abu makamancin haka ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kuros Ribas - Wata mata mai suna Maryam Zakari ta watsawa dan cikinta tafasasshen ruwan zafi kan zargin neman mata.

Wannan lamari ya faru ne a Unguwar Hausawa da ke Calabar cikin jihar Kuros Riba inda mahaifiyar ke zargin yaron da hana ta kudin da ya ke bata.

Mahaifiya ta kona dan cikinta da ruwan zafi
Jami'an 'yan sanda ba su samu labarin faruwar lamarin ba. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Meye dalilin mahaifiyar na kona danta?

Matar wacce aka fi sani da Asabe ta kona dan nata ne mai suna Babanne Abdullahi wanda ke aikin leburanci a Kasuwar Manja don rufa wa kai asiri.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Wani Matashi Ya Buga Wa Mahaifinsa Taɓarya Har Ya Mutu Kan Ƙaramin Abu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kanin matashin da aka konan ya zargi yayan nasa da neman mata wanda hakan ya saka ba ya bai wa mahaifiyar kudi kamar a baya.

Amininya ta tabbatar da cewa wasu shaidun gani da ido sun ce mahaifiyar ta watsawa dan nata ruwan zafi wanda ya yi mummunan kona masa jiki daga mararsa har zuwa mazakutarsa.

Martani mutane kan kona dan da mahaifiyar ta yi

Majiyar ta ce:

“Ko da abin ya faru mijin da take aure mai suna Zakari ya buga wa wani amininsa waya kan ya zo ya ga abin da matarsa ta aikata.
“Nan take aka dauki matashin zuwa wani asibiti mai zaman kansa da ke Unguwar Hausawa.
“Ganin haka kuma ta sa mutane suka yi ca a kan Asabe tun daga gidan har asibiti suna neman su dauki doka a hannu amma aka hana.”

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Matashi Ya Farmaki Malamin Addinini Tare Da Ajalinsa Da Adda, An Bazama Nemanshi

Kakakin Rundunar ’yan sanda a Jihar, SP Irene Ugbo ya ce ba su samu labarin faruwar lamarin ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, cewar Vanguard.

Matashi ya buga wa mahaifinsa tabarya a Ribas

A wani labarin, wani matashi mai suna Ikechi ya haddasa tashin hankali yayin da ya halaka mahaifinsa ta hanyar buga masa tabarya a Obio Akpor da ke jihar Ribas.

Matashin ya tafka wannan danyen aiki ne bayan ya nemi mahaifinsa ya ba shi kudi, amma ya ki, bisa haka ya yi ajalinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.