“Ka Sa Hannu Kan Hukuncin Kisana”: Dan Shekaru 15 Da Aka Yankewa Hukuncin Kisa Ya Aika Sako Ga Zulum

“Ka Sa Hannu Kan Hukuncin Kisana”: Dan Shekaru 15 Da Aka Yankewa Hukuncin Kisa Ya Aika Sako Ga Zulum

  • Wani matashi da aka yankewa hukuncin kisa, Mustapha Abubakar, ya rubutawa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum da ya sanya hannu a kan hukuncin da aka yanke masa
  • Abubakar mai shekaru 15 ya ce idan Gwamna Zulum ba zai iya yi masa sassauci ba cikin kankanin lokaci, to ya rattaba hannu kan takardar kisan nasa
  • Abubakar ya yi zargin cewa tsoffin fursunoni na neman lalata da shi tare da cin zarafinsa

Jihar Borno - Mustapha Abubakar mai shekaru 15 ya rubuta wasika zuwa ga gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, da ya sanya hannu kan hukuncin kisansa.

A cewar SaharaReporters, an yankewa matashin hukuncin kisa ta hanyar rataya yana da shekaru 14 kan garkuwa don karbar kudin fansa wanda ya yi sanadiyar mutuwar wanda ya sace.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Zabe: Atiku Ya Yi Sabon Zargi a Kan Kotun Zaben Shugaban Kasa

Matashi da aka yankewa hukuncin kisa a jihar Borno
“Ka Sa Hannu Kan Hukuncin Kisana”: Dan Shekaru 15 Da Aka Yankewa Hukuncin Kisa Ya Aika Sako Ga Zulum Hoto: @AmnestyNigeria
Asali: Twitter
"A lokacin da nake cike da kuruciya, na bari kwadayi da wauta ya rude ni har na fada tarkon son yin kudi cikin gaggawa na garkuwa da mutum don samun kudin fansa domin na siya babur. Abun takaici, ba wai asiri ya tonu kawai bane, ya yi sanadiyar mutuwar wanda na sace, mutum kamar ni wanda ke da lalurar rashin lafiya ba tare da na sani ba a wancan lokacin."

Abubakar, wanda yake tsare a gidan gyara hali na Maiduguri, yana rokon a gaggauta yanke masa hukunci idan rokonsa na neman sassauci ba zai samu ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin wasikar sa mai kwanan wata 1 ga watan Satumba, 2023, ya yi zargin cewa ana cin zarafinsa sannan tsoffin fursunoni da karkatattun masu gadi na neman lalata da shi.

Matashi ya roki Zulum da ya rattaba hannu kan hukuncin kisansa

Kara karanta wannan

Rashin Tsaro: Yadda Al’umma Ke Cin Dusa Saboda Yunwa a Wata Jihar Arewa

Ya ce idan har rokon da ya yi na neman afuwa ba zai samu ba "a cikin dan lokaci", Gwamna Zulum, ya yi gaggawar sanya hannu kan hukuncin kisansa.

Kungiyar Amnesty ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta soke hukuncin kisan da aka yankewa Abubakar

Da take magana kan lamarin Abubakar, kungiyar Amnesty International ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu, Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida da Gwamna Zulum da su soke hukuncin kisan da aka yankewa matashin.

A wani rubutu da ta yi a manhajar X @AmnestyNigeria, kungiyar ta rubuta:

"Amnesty International ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gaggauta soke hukuncinkisa kan dan shekaru 15 Mustapha Abubakar wanda ke cikin wadanda aka yankewa hukuncin kisa a gidan gyara hali na Maiduguri a jihar Borno. @officialABAT @BTOofficial @ProfZulum"

Matashi ya kulle mahaifansa a daki, ya saci motarsu da wasu kayayyaki a jihar Ogun

A wani labarin, mun ji cewa wani matashi mai shekaru 17 ya fakaici iyayensa tare da tafka musu mummunan sata a jihar Ogun.

Matashin mai suna Ayomiposi Esan ya sace wayoyin salula 3 da janareta 2 da kuma mota kirar Toyota Corolla, Legit.ng ta tattaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel