Gwamnan CBN, EFCC, Hafsun Soji da Mutanen Buhari da Tinubu Ya Kora a Kwana 100
- Bola Ahmed Tinubu ya tsige wasu daga cikin shugabannin gwamnatin tarayya da ya iske a ofis
- A kwanaki 100 da ya shafe a fadar Aso Rock Villa, shugaban Najeriyan ya fatattaki wasu jami’ai
- Shugabannin sojoji da tsaro da gwamnan bankin CBN su na cikin wadanda ake yi waje da su
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya cika kwana 100 a matsayin shugaban Najeriya, a karshen Mayu ya karbi mulki daga hannun Muhammadu Buhari.
A rahoton nan, Daily Trust ta kawo jerin wasu jami’an gwamnatin tarayya da sabon shugaban na Najeriya ya tsige bayan ya gyara zama a Aso Rock.
1. Godwin Emefiele
A yammacin 9 ga Yuli 2023, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cewa ya dakatar da Godwin Emefiele daga gwamnan CBN, ya ce za a binciki babban bankin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
2. Abdulrasheed Bawa
Abdulrasheed Bawa ya rasa kujerarsa a hukumar EFCC ne a sakamakon bincike da Sakataren gwamnatin tarayya ta ce za ayi kan wasu zargi a kan shi.
3. Dr Bashir Gwandu
A makon jiya Dr. Bashir Gwandu ya rasa matsayin shugaban hukumar NASENI da Bola Tinubu ya tsige shi, ya nada matashi domin ya maye gurbin shi.
4. Lauretta Onochie
Lauretta Onochie ta na cikin wadanda canjin gwamnati ya shafa, an rusa majalisarta da ke kula da harkokin hukumar NDDC da ke aiki a yanin Neja-Delta.
5. Aliyu Abubakar Aziz
Injiniya Aliyu Abubakar Aziz ya yi kwanaki a ofis a matsayin shugaban hukumar NIMC bayan Muhammadu Buhari ya sauka, daga baya aka yi masa ritaya.
Tinubu ya canza Hafsun sojoji
6. Janar Lucky Irabor – Hafsun tsaro
7. Farouk Yahaya – Hafsun sojojin kasa
8. Awwal Gambo – Hafsun sojojin ruwa
9. Isiaka Amao – Hafsun sojojin sama
10. Usman Alkali Baba – Sufetan ‘Yan sanda
11. Babagana Monguno - Mai ba Shugabankasa shawara a kan harkar tsaro.
Bincike a EFCC
Kwanan nan aka ji labarin cafke wasu hadiman wasu Abdulrasheed Bawa; Rufa’i Zaki da Daniela Jimoh a binciken da ake yi a hukumar EFCC.
Bayanai sun kuma fito cewa DSS ta gayyaci wasu ‘yanuwan shugaban EFCC da yake tsare, an karbe wata Mercedes-Benz a hannun na kusa da shi.
Asali: Legit.ng