Ma’aikata Sun Ki Amincewa Da Tsarin Rabon Tallafi Na Gwamna Bago Na Neja

Ma’aikata Sun Ki Amincewa Da Tsarin Rabon Tallafi Na Gwamna Bago Na Neja

  • Ma’aikata a jihar Neja sun yi watsi da shirin rabon tallafi na gwamnan jihar Mohammed Umar Bago
  • Gwamnan ya tsara rabon tallafin inda ya ware ma’aikata da kuma ‘yan fansho a matsayin su na da abin yi
  • Kungiyar Kwadago ta NLC a jihar ta bukaci gwamnan ya biya Naira dubu 50 ga ko wane ma’aikaci a matsayin tallafi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Neja – Kungiyar Kwadago ta NLC reshen jihar Neja ta umarci ma’aikata su kauracewa kwamitin rabon kaya na cire tallafi.

Kungiyar ta yi fatali da tsarin da gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago ya yi inda ta ce ma’aikata da ‘yan fansho na cikin wani yanayi a jihar.

Ma'aikata sun yi watsi da tsarin rabon tallafi a Neja
Ma’aikata Sun Yi Fatali Da Tsarin Rabon Kayan Tallafi A Jihar Neja. Hoto: Umar Bago.
Asali: Facebook

Meye kungiyar ma'aikatan ke cewa a Neja?

Shugaban kungiyar a jihar, Idrees Lafene da takwaransa na kungiyar TUC, Ibrahim Gana ne su ka bayyana haka a jiya Litinin 4 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Sharrin Kishi: Mutumi Ya Aika Hoton Tsohuwar Buduwarsa Tsirara ga Mai Neman Aurenta

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun yi watsi da tsarin gwamnan inda su ka ce ya cire ma’aikata da ‘yan fansho a cikin wadanda za su ci gajiyar tallafin, The Nation ta tattaro.

Su ka ce:

“Yadda gwamnatin Neja ta tsame ma’aikata da ‘yan fansho da gangan a tsarin rabon tallafi ya tayar da kura a kungiyar wanda ka iya kawo tsaiko a aikin gwamnati.
“Wannan tsari na cire ma’aikatan ba zai haifar da 'da mai ido ba kuma ba za mu yarda ba ganin yadda kullum mu ke aiki don samarwa jihar kudaden shiga.”

Wane shawara su ka bai wa gwamnan Neja?

Sun shawarci gwamnan da ya saka ma’aikata a cikin rabon don rage musu wahalhalun da su ke ciki a yanzu.

Har ila yau, kungiyar ta bukaci gwamnan da ya ware Naira 50,000 ga ko wane ma’aikaci yayin ganawarsu tare da mika bukatunsu guda tara, EkoHotBlog ta tattaro.

Kara karanta wannan

Daga Karshe: Abba Gida-Gida Ya Lashi Takwabin Aurar Da 'Yar Da TikTok Murja Kunya

Ta ce:

“Daga cikin bukatun akwai biyan Naira dubu 50 ga ma’aikatan jihar da kananan hukumomi a matsayin tallafi da kuma biyan Naira dubu 30 ga ‘yan fansho na jihar gaba daya.
“Sauran sun hada da kayyade farashin kayayyaki da samar da tsaro da kuma gyara ma’aikatu a jihar.”

Gwamna Bago Na Neja Ya Shawarci Mutane Kan Yawace-Yawace

A wani labarin, Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja, ya bukaci al’ummar yankin Kagara da su takaita yawan zirga-zirgarsu tare da bai wa jami’an tsaro hadin kai.

Bago ya ba da wannan shawarar ne a lokacin da ya kai ziyarar barka da Sallah ga Sarkin Kagara, Malam Ahmed Garba Gunna (Attahiru ll), a fadarsa da ke Kagara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.