Farashin Iskar Gas Ya Tashi Da Kaso 9 Yayin Da Ake Tsaka Da Shan Wahalar Tsadar Man Fetur
- Farashin iskar gas ma ya tashi da kaso kusan 9 cikin dari kamar yadda man fetur ya hauhawa a kwanakin baya
- A yanzu ana siyar da ko wane kilogiram na gas Naira 745 wanda a baya bai wuce Naira 680 ba ko wane kilogram daya
- Wannan na zuwa ne bayan tashin farashin man fetur da ya jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa
FCT, Abuja – Yayin da ake ta murna cewa farashin iskar gas na saukowa, ashe abin lokaci ya ke jira.
Farashin gas ya tashi da kusan kaso 9 zuwa Naira 745 kan ko wane kilogiram daya yayin da ‘yan Najeriya ke kara shiga halin wahala, Legit.ng ta tattaro.
Meye kungiyar dillalan gas ke cewa?
Shugaban kungiyar masu siyar da iskar gas (NALPGM), Olatunbosun Oladapo ya bayyana cewa ‘yan kasar za su fara biyan karin kudin gas daga tsakiyar watan Agusta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Oladapo ya ce hakan bai rasa nasaba da tsadar man a kasuwannin duniya da kuma kudin shigo da man har ma da tsadar Dala, cewar The Sun.
Ya ce duk da yawan karbar kudade na shigo da man da kuma biyan haraji hakan bai kara farashin ba a baya saboda yadda siyan gas din ya ragu sosai.
Ya kara da cewa hakan abin takaici ne ganin yadda abin zai shafi dukkan masu harkar manya da kanana.
Yadda farashin gas din ya ke a Najeriya
Ya ce:
“Masu siyan gas a Najeriya na cikin mawuyacin hali na rashin iya siyan iskar gas yanzu don yin abinci.”
Yadda farashin iskar gas din ya ke:
1. 50kg – N37,000 wanda a baya N34,000 ne
2. 25kg – N18,500 a baya N17,000
3. 20kg – N14,800 a baya N13,600
4. 15kg – N11,100 a baya N10,300
5. 12.5kg – N9,250 a baya N8,500
6. 10kg – N7,400 a baya N6,800
7. 6kg – N4,450 a baya N4,080
8. 5kg – 3,700 a baya N3,400
9. 3kg – N2,250 a baya N2,040
Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan kasar ke murnan cewa farshin iskar gas ya yi kasa idan aka kwatanta da na man fetur.
Tinubu Zai Siyar Da Litar Gas Naira 250
A wani labarin, Shugba Bola Tinubu ya sanar da siyar da iskar gas a kan Naira 250 a kan ko wace lita daya.
Hadimin shugaban, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka yayin hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce sun shirya kawo sauki a kasar.
Asali: Legit.ng