Buhari Ya Ce Gwamnatinsa Ta Yaki Cin Hanci A Najeriya Wanda Ba A Taba Yi Ba

Buhari Ya Ce Gwamnatinsa Ta Yaki Cin Hanci A Najeriya Wanda Ba A Taba Yi Ba

  • Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi zazzafan martani kan cin hanci da rashawa a Najeriya
  • Buhari ya bayyana yadda gwamnatinsa ta yaki cin hanci da rashawa a kasar fiye da ko wace gwamnati da aka taba yi
  • Ya yi wannan martani ne kan korafe-korafe da tsohon ministan shari'a, Mohammed Adoke ya yi kan gwamnatinsa na cin hanci

FCT, Abuja - Yayin da ya ke martani kan tsohon ministan shari'a, Mohammed Adoke, tsohon shugaban kasa, Buhari ya yabi gwamnatinsa na kare kasar kan cin hanci.

Buhari ya ce nasarorin da gwamnatinsa ta samu ba a taba ganin irin shi ba a tarihin gwamnatocin kasar, Legit.ng ta tattaro.

Buhari ya bayyana yadda ya kare Najeriya daga cin hanci
Buhari Ya Yi Martani Kan Matsalar Cin Hanci A Najeriya. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Meye Buhari ya ce kan cin hanci?

Yace sun yaki cin hanci da rashawa fiye da ko wace gwamnati da aka taba yi kasar tun bayan dawowar dimokradiyya a shekarar 1999.

Kara karanta wannan

Za A Iya Binciken Buhari Da Tsofaffin Shugabanni, A Kuma Canzawa Najeriya Sabon Suna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa, Garba Shehu a jiya Lahadi 3 ga watan Satumba.

Ya ce korafe-korafen da tsohon ministan shari'a, Adoke ya yi sun samo asali ne daga gwamnatin da ya kasance a ciki.

Adoke shi ne ministan shari'a a gwamnacin tsohon shugaban kasa, Dakta Ebele Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP.

Tinubu zai kara albashin alkalai don yaki da cin hanci

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sha alwashin karin albashin alkalai don dakile cin hanci da rashawa a kasar.

Tinubu ya ce wannan ne kadai hanyar dakile cin hanci don tabbatar da ingantacciyar rayuwa ga 'yan kasa inda ya ce gwamnatinsa ta himmatu wurin kawo karshen matsalar.

Bola ya bayyana haka ne ta bakin hadominsa, Ajuri Ngelale a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a 25 ga watan Agusta, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Jero Dabarun da Za Ta Bi Domin Gyara Tattalin Arzikin Najeriya

Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Sojoji A Neja

A wani labarin, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kisan sojoji da aka yi a jihar Neja.

Buhari ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa, Garba Shehu inda ya ce ya na da tabbacin nasara daga bangaren jami'an tsaro kan 'yan ta'adda.

Wannan martani na zuwa ne bayan 'yan ta'adda sun shammaci sojoji tare da hallaka da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel