“Tana Ba Da Jikinta Don Samun Maki a Makaranta”: Ango Ya Fasa Auren Amaryarsa Kwanaki Kadan Kafin Bikinsu

“Tana Ba Da Jikinta Don Samun Maki a Makaranta”: Ango Ya Fasa Auren Amaryarsa Kwanaki Kadan Kafin Bikinsu

  • An fasa wani bikin aure da ya kamata a yi a ranar 23 ga watan Satumba bayan angon ya gano irin rayuwar da amaryar ta yi a baya mara kyau
  • Hakan ya kaance ne bayan aminin angon, wanda ya zauna gida daya da amaryar a lokacin da take jami'a, ya fadi duk abun da ya gani a shekarun baya
  • Ya tona yadda amaryar ke ba da jikinta domin samun maki a jami'ar ABSU da kuma yadda take bin maza

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mutumi ya soke aurensa da wata tsohuwar dalibar jami'ar Abia (ABSU) bayan ya samu labarin mummunan rayuwar da ta yi a baya.

Wata budurwa mai suna Chichi, ta wallafa a manhajar X cewa ya kamata a yi bikin a ranar 23 ga watan Satumba kuma ta shirya halartan wannan biki.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Makale a Birtaniya Bayan Matarsa Da Ke Cin Amanarsa Ta Soke Bizarsa Don Auren Wani Daban

Tana amfani da jikinta wajen samun maki lokacin da take makaranta
An yi amfani da horon don misali ne kawai. Wadanda ke hoton ba su da alaka da batun da ake magana kansa a rahoton. Hoto: Zave Smith Photography, Fotografic Inc, Dann Tardif
Asali: Getty Images

Aminin ango ya tona irin rayuwar da amarya ta yi a baya

A cewar Chichi, aminin angon ya zauna a gida daya da amaryar mai shekaru 30 lokacin da suke jami'ar jihar Abia (ABSU) na tsawon shekaru uku kuma ya ga duk abubuwan da ta yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Aminin angon ya bayyana yadda amaryar take ba da jikinta domin samun maki da kuma yadda ta zubar da cikin da ta samu.

Ya kuma fallasa yadda ya kwanta da ita sannan ya bai wa abokansa ita don yin badala. Angon ya kuma soke auren duk da rokon da amaryar ta yi masa.

Chichi ta rubuta:

"An soke auren da ya kamata na halarta a ranar 23 ga watan nan.
"Menene dalili? aminin ango ya zauna gida daya da amaryar a Absu.
"Ya ga komai da amaryar ta yi na tsawon shekaru uku.

Kara karanta wannan

Jami’in Dan Sanda a Adamawa Ya Sharbi Kuka Wiwi Bayan An Sallame Shi a Aiki, Bidiyon Ya Yadu

"Zubar da ciki, bin maza, harma yana bayar da ita don yin badala, yadda take ba da jikinta don samun maki a makaranta. Yadda ya kwanta da ita don sanin yaya dadinta yake kafin ya yi wa wasu abokansa hanyarta. Ya yi wa yarinyar farin sani.
"A takaicen takaitawa, ya fada ma abokinsa komai duk da rokon yarinyar. Gayen ya soke auren.
"Shi da abokin suna nan tare.
"Yarinyar ce ke cikin wani hali, shekarunta 30. Bata daukar waya, bata fitowa.
Shin gayen ya yi abun da ya kamata?"

Ga wallafarta a kasa:

Jama'a sun yi martani yayin da aka fasa auren tsohuwar dalibar ABSU

@SweetMOMdee ta ce:

"Ya yi abun da ya dace. Da farko saboda shima yana da alaka da ita. Ya kamata irin abu haka su dunga fitowa fili. Abokinsa zai rike sa a zuciya idan ya gano bayan auren cewa gayen na da abu da ya shiga tsakaninsu da matarsa kuma ya boye.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Arewa Ya Ba Da Umarnin Rufe Makaranta Saboda Mummunan Laifin Da Aka Aikata a Cikinta

"Abun bakin ciki ne amma har in dai bai yi karya ba."

@Nasoebe2 ya ce:

"Wato shi gayen tsarkakke ne, idan mata na gano rabin abubuwan da gayu suke yi kafin su nemi aurensu harma da bayan sun yi aure da aure da yawa ba za su yiwu ba ko su wuce rana daya ba."

@focus1030 ta ce:

"Abun takaici ne abun da mata yake cikawa a kullun idan alaka ta yi tsami. Bana goyon bayan mace ta yi rayuwar rashin tarbiya, amma wanene tsarkakke a tsakanin su uku?"

Bayan shekaru uku a Turai, yar Najeriya ta dawo ga saurayinta bakanike

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani bakaniken bakin hanya mai suna Segun, ya cika da farin ciki yayin da budurwarsa, wacce ya dauki nauyin karatunta zuwa kasar Birtaniya ta dawo bayan shekaru uku.

Wani mai watsa shirye-shirye a TikTok Theo Ayoms, wanda ya taimaka wajen sake hada su, ya wallafa bidiyon mai tsuma zuciya a soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng