Gwamnatin Tinubu Ta Jero Dabarun da Za Ta Bi Domin Gyara Tattalin Arzikin Najeriya
- Olawale Adebayo Edun ya fadi hanyoyin da gwamnatinsu za ta bi wajen farfado tattalin arziki
- Ministan ya na ganin ya zama dole a takaita cin bashi, a dukufa wajen cika lalitar gwamnatin kasar
- Edun ya ci buri da babban bankin CBN, ya na so manufofin CBN su taimakawa tsare-tsaren na su
Abuja - Olawale Adebayo Edun ya kira taron manema labarai inda ya yi bayanin manufofin gwamnatin Bola Tinubu a kan tattalin arzikin kasa.
Tashar TVC ta rahoto ministan kula da tattalin arzikin Najeriya, Olawale Edun ya na mai cewa gwamnati za ta rage bada karfi wajen karbo bashi.
A maimakon neman aron kudi, Najeriya za ta karkata ga yadda za a samu karin kudin shiga musamman bayan an kafa gwamnin tarayya.
Za a daina facaka da baitul-mali
Wale Edun ya shaida cewa za su yi kokari wajen toshe kafofin facaka a gwamnati domin a iya kashe dukiyar al’umma ta hanyoyin da su ka dace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin yadda za a bi wajen cin ma wannan buri, akwai amfani da na’urori da fasahohin zamani yayin da ake kukan an karbi kasar a mugun yanayi.
...Gudumuwar bankin CBN
Rahoton ya ce ministan ya na sa rai babban bankin CBN zai bada gudumuwa da dabarun da za su jawo a rika samun shigowar kudin kasashen waje.
Edun wanda ya na cikin ministocin da su ke da babban aiki a gabansu ya na mai sa rai nan gaba kadan mutane za su ga amfanin cire tallafin man fetur.
Ministan ya na ganin aron dala biliyan uku da NNPC ya karbo daga bankin Afrexim zai taimaka wajen farfado da darajar Naira a kasuwar canji.
Tattalin arziki: Sauran jami'an gwamnati
Ministan kasafin kudi, Atiku Abubakar Bagudu ya na wajen a lokacin da ministan tattalin arzikin ya ke shaidawa duniya irin dabarun da za su bi.
A bangarensa, Taiwo Oyedele ya yi bayanin yadda gwamnatin kasar za ta samu karin kudin haraji, su ka ce za ayi amfani da ‘yan kasuwan da ke kasar.
Gwamnati mai-ci za ta rage talauci ta hanyar samar da abinci da ayukan yi tare da budewa mata da matasa dama da kuma rage jahili cikin al’umma.
Sabon shugaba a NASENI
Rahoto ya zo cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya tsige shugaban hukumar NASENI, an yi waje da Dr. Bashir Gwandu kafin wa’adinsa ya kare.
Ajuri Ngelale ya sanar da cewa Shugaban kasa ya yi sabon nadin mukami dazu, Malam Khalil Suleiman Halilu zai karbi jagorancin hukumar kasar.
Asali: Legit.ng