Matar Sanata Francis Alimikhena Ta Koma Ga Mahaliccinta

Matar Sanata Francis Alimikhena Ta Koma Ga Mahaliccinta

  • An yi babban rashi a jihar Edo na matar Sanata Francis Alimikhena wanda ga wakilci Edo ta Arewa a majalisar dattawa ta 10
  • Marigayiya Monica Alimikhena ta yi bankwana da duniya a ranar Alhamis, imda aka sanar da rasuwarta a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumban 2023
  • Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu wanda ya sanar da rasuwarta, ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga sanatan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Birnin Benin, jihar Edo - Monica Alimikhena, matar Sanata Francis Alimikhena, ta riga mu gidan gaskiya.

Legit.ng ta rahoto cewa an sanar da rasuwar Monica ne a ranar Juma'a, 1 ga watan Satumban 2023.

Matar Sanata Francis Alimikhena ta rasu
Sanata Francis Alimikhena ya yi rashin matarsa, Monica Alimikhena Hoto: Rt. Hon. Comrade Philip Shaibu, Prince Clem Ikanade Agba
Asali: Facebook

Marigayiya Monica ta yi bankwana da duniya ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta.

Matar Sanata Francis Alimikhena ta rasu

Francis Alimikhena ya rasa kujerar sanatansa ta Edo ta Arewa a hannun Adams Oshiomole na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a babban zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Babban Jigo Kuma Ko'odinetan Yakin Neman Zaben Shugaban Ƙasa Ya Sauya Sheƙa Zuwa PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanai ba su gama fitowa ba sosai kan rasuwar matar sanatan na majalisar dattawa ta tara, amma mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya sanar da labarin rasuwarta a shafinsa na Facebook.

A saƙon ta'aziyyar da mataimakin gwamnan ya aike ga sanata Francis, ya rubuta cewa:

"Na yi baƙin cikin rasuwar matar Sanata Francis Alimikhena, Monica Alimikhena. Ina miƙa saƙon ta'aziyyata a gareka da iyalanka a wannan lokaci mai matuƙar wahala."
"Na san marigayiya Monica na tsawon shekaru, sannan kirkinta, dattaku da hazaƙarta suna matuƙar burgeni. Matar aure ce ta gari, uwa da kaka, sannan duk waɗanda suka santa za su yi matuƙar kewarta."
"Na san cewa kalmomi sun yi kaɗan su bayyana raɗaɗin da kake ji a halin yanzu, amma ina son sanar da ke cewa muna tare da kai. Ina tare da kai, sannan zan baka duk gudunmawar da zan iya. Ina miƙa saƙon ta'aziyyata."

Kara karanta wannan

Rashin Daraja: Matashi Ya Halaka Mahaifinsa Mai Shekara 100, Kan Wani Abu 1 Rak Da Ya Yi Masa

Tsohon Sanata Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa an yi rashin babban tsohon Sanata a Najeriya, Sanata Annie Okonkwo.

Sanata Okonkwo wanda ya wakilci Anambra ta Tsakiya a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011, ya rasu ne yana da shekara 63 a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng