Hukumar NSCDC Ta Kama Wasu Mutane 46 A Gidan Gala A Jihar Gombe
- Jami’an tsaro sun kama wasu a gidajen Gala a cikin birnin Gombe bayan kafa doka a jihar
- Wannan na zuwa ne bayan gwamnan jihar, Inuwa Yahaya ya umarci kulle dukkan gidajen Gala
- Legit.ng Hausa ta tattauna da wasu kan wannan mataki na gwamnan da kuma kamen da aka yi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Gombe – Jami’an tsaro na NSCDC a jihar Gombe sun cafke wasu mutane 46 da ake zargi da karya dokar hana gidajen Gala a Gombe.
Daga cikin wadanda aka kaman akwai maza 32 sai kuma mata 14 da ake zargin karya dokar da gwamnan jihar ya kafa na kulle irin wadannan gidajen masha’a.
Meye NSCDC ta ce kan kamen a gidajen Gala?
Yayin gabatar da wadanda aka kaman a ranar Talata 29 ga watan Agusta a Gombe, kakakin NSCDC, Mu’azu Sa’id ya ce an kama su ne yayin aiwatar da su ke badala a gidajen Gala.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
“Wadanda ake zargin an kama su ne su na aikata masha’a da rashin da’a a gidajen Gala.
“Hukumar mu ta samu wasu daga cikin iyayensu sannan kuma za mu tura su zuwa kotu don musu shari’a.”
Ya kara da cewa bayan ba da umarnin da karfe 4:00 na yamma, an kama wadanda ake zargin da misalin karfe 9:00 na dare, Tori News ta tattaro.
Legit.ng Hausa ta tuntubi wasu mutane kan kulle gidajen Galan a Gombe.
Muhammad Adamu ya ce wannan gaskiya abu ne mai kyau saboda zai rage tabarbarewar tarbiya da ake fama da shi musamman tsakanin matasa.
Ya shawarci masu gidajen Galan su siyar da gidajen nasu don samun jari da kama wata sana’a daban.
Wani da bai so a ambaci sunansa ba ya ce:
“Su masu gidajen Galan shikenan sun rasa sana’arsu? ta yaya za su ci gaba da rayuwa a wannan lokaci da ake ciki na matsi.”
Yayin da wata matsashiya Aisha Hussaini ta ce matakin gwamnan ya yi dai-dai saboda zai rage yawan lalacewar al’umma inda ta ce su kuma sai su kama wata sana’a ta daban a rayuwa.
Meye shugaban masu gidajen Galan ke cewa?
Daga cikin gidajen da aka kai samame akwai Sabon Gida da ke BCGA da Jami’ar Gidan Gala a mil shida sai Gidan Wasa a mil uku da kuma yankin Liji.
Da ya ke zantawa da manema labarai, shugaban masu gidajen Gala, Usman Muhammad wanda shi ma an kama shi ya ce su na samun kudin shiga don ci da iyalansu.
Ya ce hatta matan da ke zuwa wurin su na samun na kashewa saboda su su ke rike da kansu da iyalansu, cewar Punch.
Wadannan gidajen Gala su na fadakar da mutane saboda muna wasan kwaikwayo inda ya ce ko wane wata ya na biyan ‘yan matan Naira dubu 50.
Inuwa Yahaya Ya Ba Da Umurnin Rufe Gidajen Gala Da Ke Gombe
A wani labarin, Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya ba da umarnin rufe dukkan gidajen Gala a Gombe.
Wannan na zuwa ne bayan samun korafe-korafe daga jama'a ganin yadda tarbiya ke kara tabarbarewa.
Asali: Legit.ng