Shugaban Alkalai Na Dibar Makudan Kudade Fiye Da Kashim, Akpabio, RMAFC
- Hukumar Rarraba Kudaden Shiga, RMAFC ta ce shugaban alkalan Najeria ya fi manya-manyan ‘yan siyasa samun albashi a kasar
- Hukumar ta ce shugaban alkalan na samun kudi a kasar fiye da mataimakin shugaban kasa da kuma shugaban majalisar Dattawa
- Wannan na zuwa ne bayan Kungiyar Lauyoyi ta NBA, ta bukaci karin albashi saboda irin halin kunci da su ke ciki a gudanar da shari’a
FCT, Abuja – Hukumar Rarraba Kudaden Shiga a Najeriya (RMAFC) ta bayyana cewa Shugaban Alkalan Najeriya (CJN) ya fi mataimakin shugaban kasa samun albashi.
Hukumar ta kuma bayyana cewa shugaban alkalan ya fi shugaban majalisar Dattawa samun kudi, The Nation ta tattaro.
Meye RMAFC ta ce kan albashin Kashim, Akpabio?
Hukumar ta bayyana haka ne yayin da tace alkalai a kotun koli na Najeriya sun fi sanatocin kasar diban albashi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wannan na zuwa ne bayan jama’a da dama na tunanin cewa masu rike da mukaman gwamnati sun fi kowa samun kudi a kasar.
Kwamishinan hukumar a jihar Kano, Farouk Abubakar ya yi karin haske kan karin albashi na alkalai yayin babban taron kungiyar lauyoyi a Abuja.
Abubakar ya ce lauyoyi da masu rike da mukaman gwamnati za su samu karin kudi na kashi 144 da hukumar da amince da shi.
Sabanin RMAFC, Meye NBA ta ce na karin albashi?
Yayin taron da aka gudanar a Abuja, Kungiyar Lauyoyi a Najeriya (NBA) ta nemi karin abashi ga shugaban alkalan Najeriya da alkalan jihohi da sauran masu aiki a bangaren shari’a.
Kungiyar ta ce bukatar karin kudin ya zama dole duba da yadda ake cikin mawuyacin hali inda ta ce idan babu walwala ‘yan kasar ba za su samu adalci a shari’a ba, cewar Thisday.
Ta kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta samar da wata hukuma ta daban da za ta kula da karin albashi na ma’aikatan shari’a a kasar baki daya.
Albashin Wasu Hukumomi Ya Fi Na Shugaban Kasa, RMAFC
A wani labarin, Hukumar RMAFC mai alhakin yanke albashin ma’aikata da ‘yan siyasa a Najeriya, ta dage a kan batun yin karin albashin ga ‘yan siyasa.
Rahotanni sun tattaro cewa shugaban RMAFC na kasa, Mohammed Shehu ya kare matakin nan da suka dauka, yace bai dace wani ya fi shugaban kasa albashi ba.
Asali: Legit.ng