Shugaba Tinubu Zai Biya Mazauna Abuja Da Za Su Rasa Filayensu Diyyar N825m
- Gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta sanar da biyan diyyar N825m a mazauna yankin Jiwa na Abuja
- Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike shi ne ya sanar da hakan bayan kammala tattaunawa da takwaransa na sufurin jiragen sama, Festus Keyamo
- Wike ya bayyana cewa diyyar N825m za a biya ne ga ƴan asalin Abuja waɗanda za su rasa filayensu saboda ginin hanyar titin jirgin sama da za a yi.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu ta sanar da shirin biyan diyyar N825.8bn ga ƴan asalin Abuja, domin yin aikin ginin titi na biyu na jirgin sama a tashar filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
A cewar Channels tv, ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike shi ne ya sanar da hakan a ranar Talata, 29 ga watan Agusta.
Dalilin da yasa Shugaba Tinubu zai biya diyya
Sanarwar na zuwa ne bayan kammala ganawa tsakanin Wike da takwaransa, Festus Keyamo, ministan sufurin jiragen sama, jami'an ma'aikatun da wakilan ƙauyen da lamarin ya shafa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya bayyana cewa N825m za ta ƙara wa mazauna ƙauyen ƙarfin gwiwar tashi daga wajen da samun haɗin kansu wajen cimma nasarar aikin ginin titin mai tsawon kilomita 4.2.
Ya kuma sanar da cewa gwamnati za ta kuma gina gada mai tsawon kilomita 5 a ƙauyen Tunga Madaki da gina asibiti na zamani.
Bayanan diyyar N825.819m da Shugaba zai biya
Wike ya buƙaci ƴan kwangila da su gaggauta dawowa wajen domin cigaba da aiki, inda ya bayyana cewa za a fitar da kuɗaɗen da aka amince da su a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta.
Sanarwar dai na zuwa ne ƙasa da sati biyu bayan an rantsar da tsohon gwamnan na jihar Rivers a matsayin ministan birnin tarayya Abuja.
Hadimin Atiku Ya Fadi Iya Wa'adin Da Ya Ragewa Bola Tinubu a Kan Kujerar Shugabanci, Ya Ba Shi Shawara
Tun da farko mazauna ƙauyen na Jiwa, sun fara tattaunawa da gwamnatin Najeriya kan za ta biya N2.5m a matsayin diyya kan kowacce kadada ɗaya.
Wike Ya Kawo Sabon Tsari a Abuja
A wani labarin kuma, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike ya dawo da tsarin tsaftace birnin na Abuja.
Wike ya bayyana cewa a sabon tsarin, za a riƙa aikin tsaftace birnin sau biyu a duk wata, kuma tuni har ga gayawa Shugaba Tinubu wannan sabon tsarin na sa.
Asali: Legit.ng