Nyesom Wike Ya Dawo Da Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Da Ake Yi a Birnin Tarayya Abuja

Nyesom Wike Ya Dawo Da Tsaftar Muhalli Na Wata-Wata Da Ake Yi a Birnin Tarayya Abuja

  • Ministan babban birnin tarayyar Najeriya Nyesom Wike, ya dawo da tsarin tsaftace muhalli a birnin
  • Wike dai ya dawo da tsarin da ake yi na wata-wata domin tabbatar da tsaftar birnin na Abuja
  • Ya bukaci mazauna birnin da su bai wa gwamnati haɗin kai domin samun nasarar abinda aka tasa gaba

FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Ezenwo Wike, ya ce ya gama yanke shawarar dawo da tsarin tsaftace muhalli na wata-wata a babban birnin tarayya Abuja.

Wike ya bayyana hakan ne a Abuja bayan kammala taro da 'yan kwangilar da ke tafiyar da ayyuka daban-daban a cikin birnin.

Wike ya dawo da tsohon tsarin tsaftace muhalli na Abuja
Nyesom Wike ya dawo da tsarin tsaftace muhalli na wata-wata a Abuja. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Yadda tsarin tsaftace muhallin da Wike ya zo da shi yake

Wike ya bayyana cewa ya riga da ya shaidawa Shugaba Bola Tinubu cewa za a riƙa yin tsaftar muhallin ne aƙalla sau biyu a kowane wata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Gana da Minista 1 Kan Muhimmin Batu a Villa, Bayanai Sun Fito

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wike ya ce ya shaidawa Tinubu cewa za a ware ranakun Asabar biyu na kowane wata daga ƙarfe 7 na safe zuwa ƙarfe 10 na safe domin kowa ya samu damar tsaftace muhallinsa.

Ya kuma ƙara da cewa hakan zai bai wa kamfanonin kwashe shara damar zuwa kasuwanni da sauran wuraren taruwar jama'a domin kwashe sharar da aka tara.

Wike ya nemi mazauna Abuja su ba da haɗin kai

Ministan ya kuma ce domin tabbatar da cewa an samu damar tsaftace birnin na tarayya, akwai buƙatar kowane mazaunin na Abuja ya bada gudummawarsa.

Ya bukaci mazauna Abuja da su yi ƙoƙarin ware sa'o'i uku a ranakun tsaftar wajen tattaro duk wata shara da suke da ita domin ma'aikatan muhallin su samu damar kwashewa.

Daga ƙarshe Wike ya ƙara jaddada cewa za su kawar da duk wasu gine-gine da aka yi ba bisa ka'ida ba, domin dawo da birnin yadda yake tun asali kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wike Ya Bayar Da Umarnin Cafke Mamallakin Benen Da Ya Rufto a Birnin Tarayya Abuja

Shehu Sani ya shawarci Wike ya koma jam'iyyar APC

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan shawarar da tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bai wa Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya.

Shehu Sani ya shawarci Wike ya koma jam'iyyar APC saboda ya samu damar yi ma ta aiki yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng