Kotu Ta Dakatar Da Hukumomin EFCC, CCB Daga Binciken Muhuyi Magaji
- Babbar kotun jihar Kano ta dakatar da hukumomin EFCC, CCB da ICPC daga binciken hukumar PCACC ta jihar
- Hukumomin dai sun fara gudanar da binciken shugaban hukumar Muhuyi Magaji Rimingado bisa zargin cin hanci
- Kotun ta amince da ƙorafin da gwamnatin jihar Kano ta shigar na hana hukomomin yin katsalandan cikin harkokin PCACC
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Babbar kotun jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar hukumomim EFCC, CCB da ICPC daga yin katsalandan a cikin harkokin hukumar ƙorafe-ƙorafen jama'a da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC).
Daily Trust ta rahoto cewa hukumomin EFCC da CCB a wasu wasiƙu da suka aike daban-daban ga PCACC sun buƙaci gudanar da bincike a kan hukumar
EFCC ta buƙaci darektan kuɗi na hukumar da ta gabatar da kanta tare da wasu takardu domin amsa tambayoyi a ranar Litinin, yayin da hukumar CCB ta buƙaci samun wasu takardu ne domin taimaka mata wajen binciken da take yi.
Kano: Kotu Ta Yi Hukunci Kan EFCC, ICPC Na Kama Rimingado Saboda Binciken Bidiyon Dala, Bayanai Sun Fito
Gwamnatin Kano ta shigar da ƙara
Sai dai, gwamnatin jihar ta hannun babban lauyanta, ta shigar da ƙara a gaban babbar kotun jihar domin hana yin bincike a kan yadda hukumar PCACC take gudanar da ayyukanta, cewar rahoton Vanguard.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gwamnatin ta kuma buƙaci a bayyana cewa hukumar EFCC ba ta da hurumin yin bincike kan laifukan da aka yi a matakin jiha inda akwai hukumomin da wannan nauyin ya rataya a kansu.
Kotu ta yi hukunci
A yayin da yake yanke hukuncinsa, mai shari'a Farouk Lawan Adamu, ya dakatar da waɗanda ake ƙara daga yin katsalandan ko ɗaukar wani mataki kan harkoki, ayyuka da lamuran waɗanda suka shigar da ƙara.
Waɗanda ake ƙarar dai su ne hukumomin EFCC, CCB da ICPC, yayin da babban lauyan gwamnatin Kano, hukumar PCACC da shugaban hukumar PCACC, Muhuyi Magaji Rimingado, a ka lissafo su a matsayin masu shigar da ƙara.
Alƙalin kotun ya ɗage sauraron ƙarar har sai zuwa ranar 25 ga watan Satumba.
An Zaftare Kudin Makaranta a Kano
A wani labarin na daban kuma, gwamnatin jihar Kano, ta zaftare kuɗin da ɗalibai ke biya a makarantun gaba da sakandire mallakinta da ke a jihar.
Gwamnatin ta rage kaso 50% na kudin da ɗalibai ke biya domin rage musu raɗaɗin tsadar rayuwa da ake fama da shi a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng