Tsadar Rayuwa: Yadda Garin Kwaki Ya Halaka Wata Yarinya Tare Da Galabaita Yan Uwanta 5 a Kano

Tsadar Rayuwa: Yadda Garin Kwaki Ya Halaka Wata Yarinya Tare Da Galabaita Yan Uwanta 5 a Kano

  • Wasu iyali a yankin karamar hukumar Tarauni da ke jihar Kano sun gamu da ibtila'in rayuwa sakamakon matsin da ake ciki a yanzu
  • Iyalin sun rasa diyarsu daya sannan yaransu biyar suka galabaita sanadiyar cin kwadon garin kwaki
  • Rashin kudi yasa sun wuni basu ci abinci ba kafin daga bisani mahaifinsu ya kawo kwaki don maganin yunwa, suna gama ci suka barke da amai da gudawa

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da fuskantar matsin rayuwa a fadin kasar, ibtila'i ya afkawa wasu iyali a jihar Kano inda ake zargin garin kwaki ya yi ajalin wata yarinya tare da galabaita yan uwanta su biyar.

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa yarinyar mai suna Firdausi Mahmud Abdullahi ta kwanta dama sakamakon cin garin kwaki da ta yibayan ta shafe tsawon lokaci ba tare da ta aka komai a cikinta ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Ta Ba Tsohon Shugaban EFCC Bawa Damar Ganin Lauyoyi Da Yan Uwansa

Lamarin ya afku ne a unguwar Rimin Hamza da ke yankin karamar hukumar Tarauni ta jihar Kano.

Garin kwaki ya yi sanadiyar mutuwar wata yarinya a Kano
Tsadar Rayuwa: Yadda Garin Kwaki Ya Halaka Wata Yarinya Tare Da Galabaita Yan Uwanta 5 a Kano Hoto: Real Ibrahim Ebwa
Asali: Facebook

Tun bayan janye tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi, iyalai da dama sun shiga gararanba inda wasu basu iya ciyar da iyalansu yadda ya kamata.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda lamarin ya faru, mahaifin yarinyar ya yi bayani

Mahaifin marigayiyar ya sanar da Aminiya cewa da kansa ya je ya siyo garin kwakin inda ya kai wa iyalinsa domin ayi wa yara kwado su ci inda daga baya daya daga cikinsu ta gamu da ajalinta.

Ya bayyana cewa yaran suna tattare da yunwa sosai a cikinsu domin dai tun safe ya fita neman abinci amma bai samu ba har sai bayan Magariba kafin ya koma gida da garin kwaki.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Kwastomomi Sun Rage Zuwa Gida Karuwai a Kano, Gidan Magajiya Ya Dauki Zafi

A cewarsa wani ne ma ya yi masa kyautar kudi Naira 500 don haka ya siya garin domin ya kai iyalinsa ta yi wa yara yan dabaru su saka a ciki.

Sai dai kuma, suna gama cin garin sai gaba dayansu suka fita daga hayyacinsu sakamakon amai da gudawa da ta kama su.

Malam Mahmud ya ce:

"Kasancewar dare ya yi ba za mu iya tafiya asibiti ba, sai muka kira wani ma’aikacin lafiya inda ya duba su ya yi musu allurai tare da yi musu karin ruwa. Sai dai wajen misalin karfe 1:00 na dare ita Firdausi ta ce ga garinku.”

Abun da yasa ni ban ci garin kwakin ba, Malam Mahmud

Ya kuma bayyana cewa shi bai samu cin garin ba kasancewar bai da yawa ba zai ratsa su gaba daya ba. A cewarsa dudu garin gwangwani biyu ne don haka ya hakura ya bar a iyalin nasa saboda tausayinsu.

Kara karanta wannan

“Budurwarsa Ta Ba Shi Kunya”: Malamin Addini Ya Yi Tsalle Daga Ginin Bene Mai Hawa 2, Ya Mutu a Anambra

Mahaifiyar yarinyar mai suna Malama Sadiya ta ce sauran yaran biyar da suka ci abincin tare da marigayiyar su ma sun ji jiki sosai.

Ta ce:

“Gaba dayanmu muka ci garin lamarin da ya zame mana amai da gudawa. Ita Firdausi kasancewar ta fi sauran yan uwanta galabaita shi ne abin ya zo da ajalinta."

Tsadar rayuwa: Gwamnatin Kano ta rage kudin makarantun gaba da sakandare

A wani labari na daban, mun ji cewa, a kokarin da ake yi na ragewa al'umma radadin halin da suke ciki na matsin rayuwa, gwamnatin jihar Kano ta ba da umurnin rage kudaden makarantun gaba da sakandare.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya umurci dukkanin shugabannin manyan makarantu na gaba da sakandare mallakin jihar Kano da su rage kudaden da dalibai ke biya na makaranta da kaso 50 cikin dari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng