Tinubu Ya Shirya Kirkirar Sabbin Gidajen Mai 9,000 Don Samar Da Mai Cikin Sauki Madadin Fetur
- Gwamnatin Tarayya za ta samar da gidajen mai 9,000 kari a kan gidajen mai dubu goma da ake da su
- Wadannan gidajen za su na samar da gas da kuma bakin mai cikin rahusa don rage radadin cire tallafi
- Ta ce gidajen mai din za su kasance masu samar da fetur da bakin mai kuma duk a wuri daya
FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta shirya bude sabbin gidajen mai 9,000 don samar da gas daga dubu goma da ake da su a fadin kasar.
Shugaban Hukumar Bunkasa Gas ta Najeriya (NGEP), Mohammed Ibrahim shi ya bayyana haka inda ya bayyana cewa shirin ya yi nisa, Legit.ng ta tattaro.
Me ye Tinubu ke shiryawa kan mai?
Ibrahim ya bayyana haka ne yayin taron karawa juna sani kan cire tallafin mai a jihar Legas.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce wannan shiri ya sha samun tasgaro daga wasu da su ke cin moriyar tallafin mai.
Wannan na zuwa ne bayan kudaden hukumar da su ka kai Naira biliyan 250 su ka makale a Babban Bankin Najeriya, CBN saboda wasu ka'idoji.
Daily Trust ya tattaro cewa Gas ya fi araha da kuma saukin amfani ga mutane da ababan hawa bayan cire tallafin mai.
Meye Tinubu ke shirin bunkasawa?
Ya ce gwamnatin Najeriya za ta iya cire mutane miliyan 100 a talauci kamar yadda ta yi alkawari idan aka bunkasa harkar gas.
Ibrahim ya kara da cewa wannan shiri zai fara aiki ne nan da watanni shida inda zai ba wa masu ababan hawa damar amfani da gas.
Ya ce an samar da kayan aiki fiye da miliyan biyar da za su sauya injunan zuwa amfani da gas fiye da miliyan 30.
Inda ya ce hakan zai samar wa mutane aikin yi da su ka kai miliyan 12.5 a Najeriya.
Gwamnati Za Ta Sauya Amfani Da Fetur Zuwa Gas A Ababan Hawa
A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta shirya sauyawa mutane ababan hawansu zuwa masu amfani da gas ganin yadda fetur ya yi tsada.
Hukumar Koyar da Fasahar Sufuri a Najeriya (NITT) ita ta bayyana haka inda ta ce hakan zai rage tsadar mai a kasar.
Asali: Legit.ng