Allah Daya Gari Banban: Dan Najeriya Ya Saka Siket Zuwa Wajen Daurin Aurensa, Bidiyon Ya Yadu
- Wani dan Najeriya ya saka siket sai kace mace zuwa wajen auren budurwarsa farar fata, kuma bidiyon ya yadu a TikTok
- Amaryar tasa baturiya ma ta yi shigar da ba a saba gani ba inda ta saka doguwar riga da katan kwat a sama
- Masu amfani da TikTok sun taya ma'auratan murna bayan bidiyonsu ya yadu saboda yanayin shigar da suka yi a ranar aurensu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Daga karshe wani dan Najeriya ya auri sahibarsa baturiya kuma ya hakan cikin siga da ba za a taba mantawa ba.
A cikin wani bidiyon TikTok da ma'auratan suka wallafa a shafinsu, @majiq.pia, an gano su sanye da kaya da ba a saba gani ba zuwa wajen aurensu.
Bidiyon ya nuna cewa mutumin ya sanya kwat da siket zuwa wajen daurin aurensa.
"Babu Aiki": Matashi Dan Najeriya Da Ya Ciyo Bashi Ya Tafi Uk Ya Koka Kan Rashin Aikin Yi, Bidiyonsa Ya Janyo Cece-Kuce
Ba a san dalilin da yasa ya zabi yin irin wannan shiga ba, amma shakka babu ya so yadda ya bayyana a babbar ranarsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Dan Najeriya ya saka siket zuwa wajen aurensa
An gano matar ma sanye da doguwar riga da kwat da ya yi mata yawa.
Amma abu guda da aka lura da shi a bidiyon shine tsantsar son da ma'auratan ke yi wa junansu. Sun yi rawa yayin da suke rike da hannayen junansu.
Cike da farin ciki, matashin ya ayyana cewa a yanzu ya zama mijin aure. Farin cikinsa bai san iyaka ba.
Mutanen da suka ga bidiyon a TikTok sun bayyana cewa sun so yanayin shigarsu.
Kalli bidiyon a kasa:
Martanin jama'a yayin da dan Najeriya ya saka siket zuwa wajen aurensa
@Monica Importer ta ce:
"An halicci mutanen nan biyu don junansu ne."
@Chunli ya yi martani:
"Kun dace da juna kuma kuna cikin farin ciki."
@marysunday551 ta ce:
"Ina taya ku murna da farin cikin aurenku."
@lindaeboh ta ce:
"Na so murmushinsu. Ina taya su murnar aure."
@WISDOMWHITEJP ta ce:
"Wannan shine mafarkin kowani namiji. Na taya ka murna yarona."
Yadda juna biyu ya sauya halittar wata kyakkyawar mata ya ba da mamaki
A wani labari na daban, wata kyakkyawar mata yar Najeriya ta bai wa mutane mamaki matuka kan yadda ta koma bayan ta samu juna biyu.
Wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya ya nuno gagarumin sauyi a yanayin halittar matar watanni bayan ta samu juna biyu.
Asali: Legit.ng