An Bukaci Shugaba Tinubu Ya Ba Yankin Kudancin Kaduna Kujerar Minista

An Bukaci Shugaba Tinubu Ya Ba Yankin Kudancin Kaduna Kujerar Minista

  • Wata ƙungiya da yankin Kudancin Ƙaduna ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba yankin kujerar minista
  • Ƙungiyar Southern Kaduna Renewed Hope Movement of Nigeria ta buƙaci hakan ne bisa ƙorafin mayar da yankin saniyar ware da aka daɗe ana yi
  • Ba a bayar da muƙamin kujerar minista daga jihar Kaduna ba bayan majalisa ta ƙo amincewa da tsohon gwamna Nasir El-Rufai

Jihar Kaduna - Wata ƙungiyar siyasa mai suna Southern Kaduna Renewed Hope Movement of Nigeria, ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya tuna da yankin Kudancin Kaduna.

Ƙungiyar ta buƙaci shugaban ƙasar da ya ɗauko minista daga yankin, domin gyara abin da ta kira da mayar da yankin saniyar ware da aka daɗe ana yi, rahoton Channels tv ya tabbatar.

Yankin Kudancin Kaduna na son kujerar minista
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Ƙungiyar ta koka cewa yankin Kudancin Kaduna bai ji da daɗi ba a ƙarƙashin shekara takwas na gwamnatin All Progressives Congress (APC), wanda hakan ya sanya ba su samu muƙamai ba a matakan jiha da tarayya, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

An Kuma Yin Juyin Mulki a Wata Kasar Afrika Ta Yamma Ta Daban? Bayanai Sun Fito

Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Yusuf Kanhu, wanda ya yi wannan kiran a ranar Juma'a, ya bayyana cewa lallai kamata ya yi kujerar minista a kai ta yankin Kudancin Kaduna, saboda gwamna da kakakin majalisa duk sun fito daga yankunan Arewaci da Tsakiya ne na jihar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ƙungiyar ta kuma yi kiran shugaban ƙasar da ya duba yiwuwar ba kwamishina a hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC), kuma ɗan asalin Kudancin Kaduna, Abdulmalik Durunguwa, a matsayin minista daga yankin.

Babu minista daga jihar Kaduna

Har yanzu ba a cike gurbin minista daga Kaduna ba, bayan tsohon gwamna Nasir Ahmad El-Rufai, da aka zaɓa da farko bai samu amincewar majalisa ba.

El-Rufai yana da daga cikin sunayen ministoci 48 da Shugaba Tinibu ya aike zuwa ga majalisa, amma har yanzu majalisa ba ta amince da shi ba saboda rahoton da a ka bayar na tsaro a kan shi.

Kara karanta wannan

Kaico: 'Yan Bindiga Sun Bindige Malamin Addini Har Lahira a Jihar Kaduna

Bayan majalisar ta ƙi amincewa da shi, El-Rufai ya gana da Shugaba Tinubu wanda cikin ƴan kwanakin nan ya rantsar da sabbin ministoci 45, inda ya gaya masa cewa ya haƙura da zama minista, sannan ya bayar da sunan Jafaru Sani a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Tinubu Zai Gyara Albashin Alkalai

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya shirya magance matsalar cin hanci a fannin shari'a na ƙasar nan.

Shugaban ƙasar ya shirya gyara albashin alƙalai a ƙasar nan domin kawo sauyi kan yadda wasunsu ke amsar na goro wajen yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng