Tashin Hankali Yayin da Amarya Ta Yanke Jiki Ta Mutu a Ranar Aurenta a Jihar Oyo

Tashin Hankali Yayin da Amarya Ta Yanke Jiki Ta Mutu a Ranar Aurenta a Jihar Oyo

  • Wata amarya mai suna Rebecca Oyedotun ta riga mu gidan gaskiya yayin da ake hada-hadar bikinta
  • Amaryar ta yanke jiki ta yanke jiki ta fadi yayin da ake shagalin wankar amarya tare da kawayenta
  • An kwashe ta zuwa asibiti inda a nan ne rashin lafiyar tata ta kara tabarbarewa har ta tace ga garinku

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Oyo - Wata amarya mai suna Rebecca Oyedotun, ta yanke ciki ta fadi matacciya a ranar aurenta a yankin Ogbomoso da ke jihar Oyo.

Mummunan al'amarin ya afku ne a jajiberin ranar aurenta yayin da ake bikin wankar amarya tare da kawayenta, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.

Amarya ta mutu ranar aurenta
Tashin Hankali Yayin da Amarya Ta Yanke Jiki Ta Mutu a Ranar Aurenta a Jihar Oyo Hoto: MouthpieceNGR /Nigerian Tribune
Asali: UGC

A cewar mahaifin marigayiyar, mai wa'azi Oyedotun na cocin C&S, Isale-High School, amaryar bata nuna kowani alamu na rashin lafiya ba har sai da ta fadi da misalin karfe 10:30 na safiya.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa

Kafin mutuwarta, marigayiyar za ta aure Abiodun Oluwadamilare a ranar Asabar, 19 ga watan Agusta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar kanwar amaryar, an kammala shirye-shirye tsaf kafin faruwa mummunan al'amarin.

"Iyayen angon sun yanka saniyarsu a Ogbomoso, kasancewar shine da daya tilo da suka mallaka, Abiodun, angon yana cike da farin ciki, ba tare da ya san cewa akwai mummunan al'amari tafe ba."

Yadda al'amarin ya faru ana tsaka da shagali

Koda dai mahaifiyar marigayiyar, Misis Ruth Oyedotun, ta kasa magana saboda alhinin da take ciki, mahaifinta, Oyedotun ya bayyana cewa sun kwashi amaryar zuwa asibitin LAUTECH cikin gaggawa da nufin za ta dawo a kammala shirin auren.

Ya ce:

"Mun gaggauta daukarta zuwa asibitin koyarwa na LAUTECH a Ogbomoso. Bayan wasu yan lokuta, ta farfado, sannan ta daidaita, amma zuwa yammacin Asabar, sai yanayinta ya sauya don haka ta kebe a gadon.

Kara karanta wannan

Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tsige Shugaban Fitacciyar Jam'iyya Na Ƙasa, Ta Bayyana Sunan Sabon Shugaba

"An ma nemi mu kai ta asibitin koyarwa na jami'ar Bowen don yin wasu gwaje-gwaje, wanda muka gaggauta yi.
"Angon ya suma sannan ya dungi kuka, ku barni na dauke ta.
"Mun kasance a asibitin gaba daya a ranar wannan Asabar din."

Lafiyarta ta kara tsananta har sai da ta ce ga garinku a safiyar Lahadi, rahoton LIB.

Yan bindiga sun yi garkuwa da wanda ya je kai kudin fansa a Kwara

A wani labarin, mun ji cewaw adanda suka yi garkuwa da Misis Bola Ajiboye, matar Fasto Johnson Ajiboye na cocin RCCG da ke jihar Kwara, sun sako ta.

Sai dai kuma a wani yanayi mai cike da sarkakiya, masu garkuwa da mutanen sun yi garkuwa da mutumin da aka aika domin ya kai kudin fansarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng