Naira Ta Gagara Rike Dala, Kudin Najeriya Ya Cigaba da Tangadi a Kasuwar Canji
- Tangal-tangal ba ta karewa dala ba, har yanzu kudin Najeriyan ya gaza yin wani daraja a kasuwa
- A karshen makon nan ta kai sai mutum ya tanadi fiye da N900 kafin a iya saida masa $1 a kasuwar canji
- Akwai bambanci tsakanin yadda ake saye da saida kudin ketare a kafar I & E da hannun ‘yan BDC
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - A ranar Alhamis, dillalai su ka yi hasashen tashin farashin man fetur a sakamakon karyewar da Naira ta yi a kasuwar canjin kudi.
Rahoto ya zo daga Punch cewa darajar Naira ya na cigaba da sauka musamman a kan Dalar Amurka da aka saba ciniki da shi a kasashen ketare.
Bayan saida Dala a kan N950 da aka yi a makon da ya wuce, an samu sauki a kwanakin bayan nan yayin da darajar kudin gidan ya kai N790.
Ana samun banbancin farashin kudin waje
An gaba farin cikin saukar Dalar Amurka, sai aka ji Naira ta sake sunkayawa a kasuwa, ‘yan canji sun saida Dala a kan N920 a jiyan nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Legit.ng Hausa ta fahimci akwai bambanci tsakanin farashin da ake saida kudin kasar waje a kafar I & E da kuma hannun ‘yan canji a kasuwa.
Babu cikakken gwamna a CBN
Akwai tazarar fiye da N100 tsakanin farashin masu canza kudi da kuma na bankin CBN ta kasuwar da ake warewa masu sayayya daga ketare.
Duk da halin da ake ciki, babu cikakken gwamman babban banki a Najeriya, an dakatar da Godwin Emefiele, an bar gwamna na rikon kwarya.
Dala za ta shafi farashin fetur?
Tashin darajar Dalar ya jawo dilallan mai su na dar-dar a yau domin da kudin ketaren su ke shiga kasuwar duniya su sayo tatattaccen fetur.
‘Yan kasuwa sun shaidawa Punch cewa muddin za a saida masu Dala a kan N920, babu ta yadda za su iya saida litar man fetur a kan N615-N620.
Masu shigo da fetur sun nuna ba za ta yiwu su ci riba ba sai gidajen mai sun saida litansu tsakanin N680 zuwa N700 ba saboda canjin farashin.
Linda Ikeji ta kara da cewa muddin gwamnatin tarayya ba za ta dawo da tallafin fetur ba, mafitar ita ce a saidawa dillalan mai da araha ta CBN.
Halin Tattalin arzikin Najeriya
A makon da ya gabata aka ji labari bankin CBN ya soke dokar da aka fito da ita a 2021, za a koma saida kudin waje ga ’yan canji bisa wasu ka'idoji.
Gwamnatin Bola Tinubu da ta gaji Muhammadu Buhari tayi alkawarin farfado da tattalin kuma NNPC ya karbo bashin $3bn domin tsaida Dala.
Asali: Legit.ng