Bidiyon Jarumar Fim Da Attajirin Mijinta a Wajen Bikin Diyar Sanata Sani Ya Girgiza Intanet
- Shahararriyar jarumar Nollywood Regina Daniels ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da bidiyonta da biloniyan mijita Ned Nwoko a wajen wani biki ya bayyana
- Masoya sun garzaya shafin jarumar inda suka dungi jinjina mata kan daukakar da ta samu wanda ya sha banban da na yan fim a Najeriya
- Ma'auratan sun dauki hankali a wajen bikin da aka yi a Abuja wanda yake na diyar takwaran mijinta ne, Sanata Sani
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani bidiyo na jarumar Nollywood Regina Daniels tare da biloniyan mijinta, Ned Nwoko, a wajen bikin diyar Sanata Sani ya dauka hankali
A cikin bidiyon da ya yadu, Regina ta fito shar da ita inda ta dunga walwali sannan ta kasance dauke da murmushi a fuskarta wanda ya kara fito da tsantsar kyawunta.
Jaruma Regina Daniels cikin manyan matan sanatoci
An gano jarumar tana gaisawa da sauran manyan mata da suka girme mata a wajen taron, sannan ta fito shar tamkar kifi a cikin kogi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mutane da dama a soshiyal midiya sun yaba da yanayin shigar Regina. A lokaci guda, wasu sun kwararo ruwan yabo ga jarumar kan daukakar da ta samu daga jarumar fim zuwa wata babbar mutum a cikin al'umma.
Kalli bidiyon a kasa:
Martanin jama'a kan bidiyon Regina Daniels a wajen bikin diyar Sanata Sani
@zubbyprisca042:
"Regina kadai ce ke cin duniyarta a Najeriyar nan, gaba daya sauranmu za mu dunga bayani har mu gaji ba hujja."
@simeon.delight:
"Daga Regina har Ned duk walwali suke, kwanciyar hankali da kudi suna da kyau."
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa
@moonshine_skincareng:
"Lallai kin shirya kuma horar da kanki sosai a wannan tafiyar, karin darajar a halayya, nutsuwa da yadda kike magana duk suna da kyau, sannu da kokari Gina."
@corazon_berry:
"Wahala bata da kyau gaskiya. Yar'uwa, kin yi zabi nagari."
@only_one_milly:
"Shin ku ga wannan?? MATAN SANATAOCI."
@loveaca2018:
"Regina ce kadai ta yi zabi nagari a kasar nan...smh."
Budurwa ta dauki hankali da yanayin rawanta a wajen biki
A wani labarin, mun ji cewa wata budurwa Bahaushiya ta burge masu amfani da soshiyal midiya saboda yanayin rawar da ta yi a wajen wani taro.
A bidiyon da aka wallafa a TikTok wanda ya samu mutum sama da miliyan da suka kalla, an gano matashiyar tana rawa tare da girgiza kwankwasonta yayin da wani kida ke tashi daga kasa.
Asali: Legit.ng