Hukumar Yan Sanda Ta Musanta Ikirarin Ɗan Bindiga Ya Zama Gwamna a Neja

Hukumar Yan Sanda Ta Musanta Ikirarin Ɗan Bindiga Ya Zama Gwamna a Neja

  • Hukumar 'yan sanda ta ƙaryata rahoton da ke yawo cewa wani shugaban 'yan bindiga ya ayyana kansa a matsayin gwamnan Neja
  • Kakakin 'yan sandan jihar, Wasi'u Abiodun, ya ce rahoton ƙanzon kurege ne kuma jami'an tsaro na aiki tukuru domin dawo da zaman lafiya
  • Ya kuma buƙaci ɗaukacin mazauna jihar Neja da su yi watsi da labarin wanda aka kirkira domin firgita mutane

Niger state - Hukumar 'yan sanda reshen jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya ta bayyana cewa babu wani ɗan bindiga da ya kai matsayin gwamna a jihar.

Rundunar ‘yan sandan ta faɗi haka ne yayin maida martani ga rahotannin soshiyal midiya na cewa ƙasurgumin ɗan bindiga, Dogo Geide, ya ayyana kansa a matsayin gwamnan jihar Neja.

Yan sanda sun musanta ikirarin ɗan bindiga Dogo Geide.
Hukumar Yan Sanda Ta Musanta Ikirarin Ɗan Bindiga Ya Zama Gwamna a Neja Hoto: Punchng
Asali: UGC

Rahotannin da ke yawo sun nuna cewa, Geide ya yi kira ga al’ummomi da su ba shi goyon baya kuma ya ba su tabbacin cewa zai tabbatar da tsaro da walwalar su.

Kara karanta wannan

To fah: Za a runtuma kame a wata jiha, 'yan bindiga sun sheke dan sanda, sun sace bindiga da hularsa

Menene gaskiyar wannan ikirari?

A wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a, kakakin hukumar yan sandan, Wasiu Abiodun, ya ce irin wannan furuci ya faru ne kawai a tunanin marubucin da ya kirkiiri labarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaidar Punch ta rahoto sanarwan na cewa:

"Hukumar ‘yan sandan jihar Neja na son mayar da martani ga wani labari da ke yawo a wasu kafafen sada zumunta cewa wani shahararren dan bindiga ya ayyana kansa a matsayin gwamna a jihar Neja."
"Hukumarmu na son bayani dalla-dalla cewa labarin ƙarya ne gaba ɗaya, kuma hakan mai yuwuwa ta faru a tunanin wanda ya kirkiro labarin ya rubuta."
“Tawagar jami’an tsaro na hadin gwiwa a jihar tare da taimakon gwamnatin jihar suna aiki tukuru domin magance matsalolin tsaro da ake fuskanta. An girke dakaru a wurare daban-daban."

Kakakin yan sanda ya kuma yi kira ga al'umma da su yi watsi da irin waɗannan labarai, yana mai cewa wani yunkuri ne na bata gari da nufin haifar da firgici ta hanyar farfaganda.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wanda Ake Zargi Da Hannu a Kashe Shugabar Alkalan Kotu a Arewacin Najeriya

Abiodun ya kuma bukaci 'yan jarida su guji yada irin wannan farfagandar ta kafafensu daban-daban, kamar yadda rahoto ya tabbatar.

Dalibai Na Da Hannu a Harin Fashi da Aka Kai Dakunan Mata

A wani rahoton na daban Gwamna Fubara ya bayyana waɗanda yake zargi da kai hari ɗakunan ɗalibai mata a jami'ar jihar Ribas.

Yayin da ya kai ziyara ta musamman jami'ar, gwamnan ya ce baya tunanin wasu 'yan waje ne suka kai farmakin, akwai sa hannun ɗaliban makarantar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262