Juyin Mulkin Nijar: Ana Fama Da Matsalar Ƙarancin Shanu, Tumaki Da Sauran Kayayyaki Bayan Rufe Iyakoki

Juyin Mulkin Nijar: Ana Fama Da Matsalar Ƙarancin Shanu, Tumaki Da Sauran Kayayyaki Bayan Rufe Iyakoki

  • Ana ci gaba da kokawa kan yadda ake samun ƙarancin shanu, tumaki da sauran kayayyakin amfani na yau da kullum
  • Hakan ya biyo bayan rufe iyakokin Najeriya da Nijar da hukumomi suka yi a kwanakin baya
  • Wani mai sana'ar sayar da dabbobi da Legit.ng ta sanya da shi, ya bayyana yadda suke shan wahala a kasuwanni

An samu ƙarancin shigowar abubuwa da suka haɗa da shanu, raƙuma, tumaki, dabino da sauransu daga jamhuriyar Nijar biyo bayan kulle iyakokin da aka yi.

Hakan ya biyo bayan hamɓarar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum da sojojin jamhuriyar Nijar ɗin suka yi a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

An yi ittifaƙin cewa kaso mafi yawa na dabbobin da ake yankawa a sassa daban-daban na Najeriya suna zuwa ne daga jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

Ana ci gaba da kokawa kan rufe iyakokin Najeriya da Nijar
An fara fuskantar ƙarancin dabbobi saboda rufe iyakokin Najeriya da Nijar. Hoto: Nura Zafi DanJarida Gaya
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan kasuwa sun koka saboda karancin shanu da tumaki

Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta haɗa a jihohin Najeriya da ke kusa da bakin iyakokin Najeriya da Nijar, ya nuna yadda 'yan kasuwa ke kokawa kan ƙarancin shigowar kayayyaki daga Nijar.

'Yan kasuwar shanu da sauran dabbobi da ke kasuwancinsu a jihohin Borno, Jigawa da Katsina, sun bayyana cewa adadin dabbobin da suke samu a yanzu ya ragu da aƙalla kaso 50% ko fiye ma da haka.

Wani mai suna Malam Ali Buba mai sana'ar sayar da naman shanu da aka yi hira da shi a wata mayankar dabbobi da ke Maiduguri, ya bayyana cewa a baya sukan yanka aƙalla shanu 200, amma yanzu da ƙyar suke ka iya yanka 50.

Ya ƙara da cewa shanun da suke saya kan naira 250,000 duk guda ɗaya, yanzu ya koma 300,000 zuwa 350,000 ma, wanda hakan ya janyo tsadar naman da suke sayarwa.

Kara karanta wannan

An Kuma Yin Juyin Mulki a Wata Kasar Afrika Ta Yamma Ta Daban? Bayanai Sun Fito

Kayayyakin wasu 'yan kasuwar sun maƙale kan iyakoki

Da dama daga 'yan kasuwa na kokawa kan yadda kayayyakinsu na miliyoyin nairori suka maƙale cikin motoci a bakin iyakokin Najeriya da Nijar.

Wani ɗan kasuwa Alhaji Hussaini Mai Dabino, ya koka kan yadda buhunan dabinon da ya sayo daga Nijar suka maƙale a bakin iyakokin ƙasashen biyu kamar yadda Daily Trust ta yi rahoto.

Ya ƙara da cewa mutane da dama da suka dogara da shi ne suke zaune babu abin yi saboda babu kayayyakin da za su je su kasa don su sami kuɗaɗen da za su ci gaba da gudanar da hidindimunsu.

Waɗannan abubuwan dai duk suna faruwa ne a daidai lokacin da abubuwa ke ƙara ƙamari kan yunƙurin da ECOWAS take yi na ganin ta dawo da dimokuraɗiyya a jamhuriyar Nijar.

Ana shan wahala wajen samun dabbobi

Wani mai sana'ar sayar da shanu da ke hada-hadarsa a kasuwannin kan iyakokin Najeriya, Alhaji Mustapha Asaka, ya shaidawa Legit.ng cewa suna fuskantar ƙarancin dabbobi a kasuwa tun bayan rufe iyakokin.

Kara karanta wannan

Barayin Dabbobi Da Aka Kama a Neja Sun Fadi Adadin Awakin Da Suka Sace a Cikin Shekara 5

Ya ce saniyar da ake sayarwa a kan naira 450,000 a baya, yanzu ta koma naira 500,000, kuma ga shi suna shan ɓaƙar walaha kafin su sami dabbobin da za su saya.

Ya buƙaci gwamnatin Najeriya da shugabannin juyin mulkin Nijar da su yi ƙoƙarin sasanta kansu don ganin an kawo ƙarshen wahalhalun da jama'a ke fuskanta.

Ni na hana ECOWAS tura dakaru Nijar - Tinubu

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan iƙirarin da shugaban Najeriya, kuma shugaban ƙungiyar ECOWAS, Bola Tinubu ya yi na cewa shi ne ya hana ƙungiyar ECOWAS tura dakarun yaƙi jamhuriyar Nijar.

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da tawagar malaman addinin Musulunci da ke ƙoƙarin sasanta rikicin na jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng