Tawagar da ECOWAS Ta Tura Nijar Ta Samu Ganawa da Hambararren Shugaban Kasa Mohamed Bazoum

Tawagar da ECOWAS Ta Tura Nijar Ta Samu Ganawa da Hambararren Shugaban Kasa Mohamed Bazoum

  • Lamari dai bai yi sauki ba game da juyin mulkin Nijar har yanzu, ana ci gaba da kai-komo kan yadda za a warware
  • An ruwaito cewa, an gana da hambararren shugaban kasa Bazoum a wata ziyarar tawagar kungiyar ECOWAS
  • A baya, malaman addini sun gana da shugabannin juyin mulkin Nijar a makon da ya gabata don neman mafita

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yamai, Nijar - Wakilan tawagar Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) a Yamai sun gana da hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum.

Wannan na zuwa ne a cewar wani rahoton gidan rediyon Faransa na kasa da kasa (RFI) a karshen makon nan.

Ganawar da Bazoum, a cewar gidan rediyon ta samu halartar tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar, wanda ya jagoranci tawagar ECOWAS.

Kara karanta wannan

Abun da Muka Tattauna Da Sojojin Juyin Mulkin Nijar, Malaman Najeriya

Yadda aka gana da Bazoum
ECOWAS ta samu ganawa da Bazoum | Hoto: @rfi
Asali: Twitter

Matsayar ECOWAS kan juyin mulkin Nijar

Kungiyar ECOWAS dai ta adana rundunar ko-ta-kwana, inda ta ce bata da zabin da ya wuce amfani da karfi idan har gwamnatin sojin Nijar ta ki mayar da shugaba Bazoum kan mukaminsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A karshen taron kwanaki biyu da hafsoshin tsaron kungiyar ECOWAS suka yi a Accra ta Ghana, kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS, Abdel-Fatau Musah, ya ce dakarun kungiyar na jiran odar kai farmaki Nijar ne kawai.

Bayan taron manema labarai da musa Musah ya gabatar, Burkina Faso da Mali, wadanda tun farko suka yi gargadi kan wani tsoma bakin soja a Nijar, sun tura jiragen yaki ga dakarun Nijar.

Yadda batun yake tun farko

A tun farko, gidan talabijin na Nijar ne ya bayyana sabon matakin na Mali da Burkina Faso a taimakawa sojojin juyin mulkin.

Kara karanta wannan

Wani hanzari: Majalisar ECOWAS ta dare kan lamarin Nijar, bayanai sun bayyana

A bangare guda, malaman addinin Musulunci a Najeriya sun samu damar zantawa da sojojin juyin mulki a Janhuriyar Nijar yayin da ake ci gaba da takkadama tsakaninsu da kungiyar ECOWAS.

Malaman Najeriya sun ajiye banbancin akida sun hada kai zuwa Nijar a kokarin da suke na ganin an samu maslaha tare da hana zubar jini a kasar ta yammacin Afrika.

Kamar yadda sashin Hausa na BBC ra haoto, Malaman karkashin jagorancin Sheikh Abdullahi Bala Lau, shugaban kungiyar Izallah ta Najeriya, sun zauna da sojojin juyin mulki na tsawon sa'o'i uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel