Hotunan miyagun makamai da aka samu bayan sojoji sun sheke dillalan makamai 3 a Sokoto
- Sojojin Najeriya dake garin Sabon Birni sun halaka dillalan bindigogi 3 dake safara daga Nijar zuwa Najeriya
- Dakarun sun yi amfani da bayanan sirri ne inda suka dinga bibiyar kaiwa da kawowar wadanda ake zargin sannan dubunsu ta cika
- An samu makamai irinsu bama-baman RPG da RPG, bindiga kirar AK47 da sauran ire-iren miyagun makamai
Shugaban sojin kasa na Najeriya, Manjo Janar Farouk Yahaya ya jinjinawa kokarin dakarun sojin kasan Najeriya dake aiki wurin Sabon Birni, garin da ke iyakar jihar Sokoto.
Dakarun sojin sun yi musayar wuta da wasu da ake zargin dillalan bindigogi ne kuma sun kashe mutum ukun tare da samo miyagun makamai daga wurinsu.
Wannan jinjinar na dauke ne a wata takarda da daraktan hulda da jama'a na rundunar, Birgediya Janar Mohammed Yerima ya wallafa a Twitter sannan ya mika ga manema labarai.
KU KARANTA: Har yanzu gwamnati bata tuntubemu ba, Hukumar makarantar da aka sace yara 156
Kamar yadda Yerima yace, dakarun sun yi amfani da bayanan sirri ne a kan kaiwa da kawowar dillalan bindigogin daga jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya kuma cike da nasara suka bibiyi wadanda ake zargi.
Babu kunya balle tsoro wadanda ake zargin suka fara sakarwa dakarun harbi, a take kuwa sojojin suka mayar da martani, lamarin da yasa aka kashe mutum uku a cikin wadanda ake zargin.
KU KARANTA: Rundunar 'yan sanda ta bankado kamfanin hada AK-47 a garin Jos
An bukaci sojojin Najeriya da su cigaba da ayyukansu da kuma tabbatar da toshe duk wata hanyar shigowar makamai da basu dace ba domin shawo kan matsalar tsaron kasar nan.
Abubuwan da aka samu daga mutum ukun da aka kashe sun hada da bama-baman RPG da RPG, bindiga kirar AK47 da sauran ire-iren miyagun makamai.
A wani labari na daban, wasu miyagu dauke da makamai sun kai farmaki yankunan Ikire da Apomu dake kananan hukumoniin Irewole da Isokan na jihar Osun kuma ana zargin har sun kashe mutum biyar a Ikire.
Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, 'yan fashi da makamin sun yi wa wani banki fashi a garin Apomu wurin karfe 3 na yamma kafin su karasa Ikire inda suka kashe mutum uku wuin cire kudi.
Hakazalika, wasu mutum biyu sun rasu a yankin sakamakon harbin da 'yan fashin suka dinga yi. Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, ta tabbatar da aukuwar lamarin inda tace ba za ta iya cewa ga yawan wadanda suka rasu ba.
Asali: Legit.ng