'Gyara Titunan Najeriya Ya Fi Tallafin Kayan Abinci Amfani', Yahaya Bello Na Kogi

'Gyara Titunan Najeriya Ya Fi Tallafin Kayan Abinci Amfani', Yahaya Bello Na Kogi

  • Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana cewa samar da tituna ingantattu yafi rage talauci kan ba da tallafin kudade ko kayan agaji
  • Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarar aikin hanyar Abuja zuwa Lokoja don gani da idonsa
  • Gwamnan ya samu rakiyar ministan ayyuka, Dave Umahi yayin da ya sha alwashin samar da hanyoyi masu inganci a fadin kasar

Jihar Kogi - Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya bayyana cewa samar da tituna ya fi ba da tallafi rage talauci.

Bello ya ce idan da gwamnati za ta samar da abubuwan more rayuwa da zai fi kan bata lokacinsu wurin ba da tallafin kudade.

Gwamna Yahaya Bello ya bayyana cewa gyaran tituna ya fi ba da tallafi amfani
Gwamna Yahaya Bello Na Kogi Ya Yi Martani Kan Ba Da Tallafi A Kasar. Hoto: @OfficialGYBKogi.
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ke duba ayyukan hanyar Abuja zuwa Lokoja tare da ministan ayyuka na Tarayya, Dave Umahi, Daily Nigerian ta tattaro.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Gwamnatin Tinubu Zata Gina Katafariyar Gadar Sama a Arewa Don Magance Abu 1 Tal

Me Yahaya Bello ke cewa game da tallafi?

Ya ce duk ba ta lokacinsu su ke yi na ba da tallafi ko kayan abinci inda ya ce tituna kadai ya isa ya rage talauci a fadin kasar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

"Ta hanyar gyaran tituna a fadin kasar kadai ya isa a kawar da talauci a tsakanin al'umma.
"Hakan ya fi saurin cire mutane a kangin talauci fiye da bayar da kayan agaji ko kuma tallafi."

Meye Yahaya Bello ya ce game da hanyar?

Yahaya Bello ya ce hanyar Abuja zuwa Lokoja na da matukar muhimmanci a kasa baki daya da kuma bunkasa tattalin arziki, Daily Trust ta tattaro.

Ya ce hanyar ta hada Kudu maso Gabashi, Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu da birnin Abuja da kuma yankin Arewa.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Sauki Ya Zo Yayin Da Tinubu Ya Shirya Siyar Da Litar Gas Naira 250 Madadin Fetur, Ya Tura Bukata Ga 'Yan Najeriya

Tun farko a jawabinsa, ministan ayyuka, Dave Umahi ya sha alwashin samar da hanyoyi masu karko don cin gajiyarsu na tsawon lokaci.

Ya bukaci 'yan kwangila da su kawo masa lissafin kwangilar samar da tituna masu inganci a fadin kasar.

Gwamna Yahaya Bello Na Kogi Ya Sallami Mukarrabansa 2

A wani labarin, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya kori wasu daga cikin mukarrabansa a ranar 13 ga watan Agusta.

Daga cikin wadanda ya kora din akwai kwamishinan Noma, Mista David Apeh da kuma mataimaki na musamman a ba da agajin gaggawa, Danladi Isah Yunusa

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.