Matsalar Tsaro: Najeriya Za Ta Yi Amfani Da Fasahohin Zamani Domin Kare Iyakokinta, In Ji Ministan Cikin Gida

Matsalar Tsaro: Najeriya Za Ta Yi Amfani Da Fasahohin Zamani Domin Kare Iyakokinta, In Ji Ministan Cikin Gida

  • Sabon ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya yi magana kan tsare iyakokin Najeriya
  • Ya ce samar da tsaron iyakoki na da muhimmanci wajen samun ingantaccen tsaro a ƙasa
  • Ya ce Najeriya za ta yi amfani da fasahohin zamani wajen tabbatar da tsaron iyakokin na ta

FCT, Abuja - Ministan harkokin cikin gida, Honarabul Olubunmi Tunji-Ojo, ya ce akwai buƙatar a tsare duka iyakokin Najeriya da suka haɗa da na sama, ƙasa da na ruwa saboda samun cikakken tsaro.

Ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Talata, yayin gabatar da wani taro na manema labarai kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Najeriya za ta yi amfani da fasaha wajen tsaron iyakarta
Ministan cikin gida ya ce Najeriya za ta yi amfani da fasahohin zamani wajen tsare bakin iyakokinta. Hoto: Nigeria Security and Civil Defence Corps
Asali: Facebook

Najeriya za ta yi amfani da fasahohin zamani wajen kare iyakokinta

Olubunmi ya ce akwai buƙatar Najeriya ta yi amfani da fasahohin zamani wajen ƙara inganta aikin tsaronta da ake gudanarwa a yanzu.

Kara karanta wannan

Ministocin Tsaro: Badaru da Matawalle Sun Ɗauki Alkawari, Sun Faɗi Lokacin da Za'a Ga Sauyi a Tsaron Ƙasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa ya samu umarni daga wurin shugaban ƙasa Bola Tinubu kan aiwatar da duk tsare-tsaren da suka dace wajen ganin an yi abubuwan da suka kamata.

A kalamansa:

“Muna da bukatar tabbatar da tsaron iyakokinmu, kuma dole ne mu tabbatar da cewa an tsare dukkan iyakokin da suka haɗa da na ƙasa, na sama da ma na ruwa.”
"Dole ne mu yi amfani da fasahohi domin ƙarfafa abin da muke kai a yanzu.”

Ministan ya ce za a yi gyara ɓangaren yin fasfo

Olubunmi ya kuma bayyana cewa, za su yi gyare-gyare wajen yin fasfo na zuwa ƙasashen waje musamman ma batun jinkirin da ake samu wajen fitowarsa.

Ya kuma bayyana cewa 'yan ƙasar waje da ke son shigowa Najeriya za su samu damar yin hakan cikin sauƙi muddun sun cancanta saɓanin yadda yake a baya kamar yadda This Day ta wallafa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Zai Tsamo Mutane Miliyan 136 Daga Talauci Kuma Zai Samar da Ayyukan Yi 10m, Bayanai Sun Fito

Ministan ya kuma bayyana cewa za su yi gyare-gyare a hukumar kashe gobara ta ƙasa musamman ma wajen jinkirin da ake samu yayin da aka samu rahoton gobara a wani wurin.

Hukumar kwastam ta yi bayani kan dalilin rufe iyakokin Nijar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan bayanin da hukumar kwastam ta ƙasa ta yi dangane da dalilin rufe iyakokin Najeriya da jamhuriyar Nijar.

Hukumar ta ce ba faɗa Najeriya take yi da jamhuriyar Nijar ba illa iyaka ta cika umarnin shugaban Najeriya kuma shugaban ƙungiyar ECOWAS, wato Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng