A Maida ni Wajen Mijina Inji Wanda Aka Ceto Daga Hannun ‘Dan Boko Haram

A Maida ni Wajen Mijina Inji Wanda Aka Ceto Daga Hannun ‘Dan Boko Haram

  • Rundunar sojojin Najeriya sun kutsa mafakar ‘yan ta’adda a garin Dikwa, a nan aka ceto Nkeki
  • A sanadiyyar haka aka iya kubutar da Mary Nkeki wanda ta rabu da iyayenta tun Afrilun 2013
  • Mary Nkeki mai shekara 27 da ‘ya ‘ya 2 ta na son ganin ta wajen mijinta, tsohon ‘dan Boko Haram

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Borno - Dakarun Operation Hadin Kai na sojojin Najeriya, sun yi nasarar kubutar da Mary Nkeki wanda ta kasance cikin ‘yan Boko Haram.

Punch ta ce Mary Nkeki mai shekara 27 ta na cikin ‘yan makarantar Chibok da Boko Haram su ka sace kusan shekaru 10 da su ka wuce a Borno.

Bayan an ceto wannan Baiwar Allah a farkon makon jiya, sai ta shaida cewa ta na auren wani tubabben ‘dan ta’addan kungiyar Boko Haram.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Yayin Da ECOWAS, Nijar Su Ka Gaza Samun Daidaito, Fafaroma Francis Ya Shiga Tsakani

Boko Haram
Sojoji sun yi fama da Boko Haram Hoto: Getty Images (Wannan ba shi ne asalin hoton ba)
Asali: Getty Images

A cewar Nkeki, sunan mijin na ta Adam, kuma ta ce da karfi da yaji aka aura mata shi da aka kama su lokacin da su ke jarrabawawar WAEC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sojoji sun gano ta 55 a matan Chibok

Manjo Janar Gold Chibuisi wanda ya ke jagorantar dakarun Operation Hadin Kai, ya ce a cikin ‘yan matan Chibok da ake nema, ita ce ta 55.

"Bayan an ceto ta, an yi mata gwajin lafiya a asibiti a asibitinmu. Sannan, an farfado da ita da kyau, kuma za a mika mata ta ga jihar Borno."

-Janar Gold Chibuisi

Mijin 'Yar Chibok ya mutu?

Da ta zanta da manema labarai bayan an mika ta a hannun ma’aikatar harkokin mata na jihar Borno, ta bayyana alakarta da tsohon ‘dan ta’addan.

Mary Nkeki ta ce ta zauna da Adam, kuma sun samu ‘ya ‘ya byu, amma sojoji sun ce daga baya wannan mutumi ya rasu, ta na rike da marayunsa.

Kara karanta wannan

100 sun mutu: Yanzu haka 'yan Boko Haram da ISWAP suna can suna ta kwabza yaki a Borno

A maimakon a ji ta na murnar rabuwa da mahaifin ‘ya ‘yanta, sai aka ji tsohuwar dalibar ta ne begen wanda aka tilasta mata aure a cikin jeji.

Da aka yi mata maganar aure sai ta ce ta na da miji wanda su ka tsere ta, har su ka isa inda sojoji su ka tsinto a Dikwa, har aka iya kubutar da su.

“Ina da miji na tuni. Ina auren Adam. Tare mu ka tsere daga hannun ‘yan ta’adda.”

Meyasa ake son 'Yan Boko Haram?

Wani masanin harkar tsaro ya fada mana wasu wasu tubabbun ‘yan Boko Haram ba ainihin sojin kungiyar ba ne, tilasta masu daukar makamai aka yi.

A irin haka ne mutanen da aka ribata bayan cin garinsu da yaki su kan auri wadannan mata da nufin tserewa da zarar sun samu damar hakan.

Majiyar mu ta ce wasu sun fi sha’awar zama da mazan da ake yi wa kallon ‘yan ta’adda saboda tsabagen kuzarinsu kuma su na dauke masu dawaniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng