An hangi wasu daga cikin matan Chibok a Yankin dajin Sambisa
Kusan shekaru shida kenan da sace ‘Yan makarantar Matan nan ta Chibok a jihar Borno. Yanzu mun ji cewa an ga wasu daga cikin wadannan mata a Dajin Sambisa.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto na musamman ta na cewa wasu daga cikin wadannan ‘Yan mata da su ke tsare har yanzu, su na cikin kungurmin Dajin Sambisa.
Wata daga cikin ‘Yan matan da aka sace bara, ta kuma samu ‘yanci a Ranar Lahadin da ta gabata, ta shaidawa ‘Yan jaridar cewa ta ga wasu Matan a Dajin kwanan nan.
A yau Laraba, 5 ga Watan Fubrairun 2020, wadannan Mata su ke shafe kwanansu na 2, 125 a hannun sojojin bangaren Abubakar Shekau na ‘Yan ta’addan Boko Haram.
A cikin Watan Afrilun 2014 ne ‘Yan ta’addan su ka sace ‘Yan mata 276. Daga ciki wasu 57 sun tsere daga motar ‘Yan ta’addan, sannan aka tsere da ragowar kusan 220.
A sakamakon kokarin da gwamnatin tarayya ta yi a baya, an iya ceto wasu daga cikin wadannan ‘Yan mata. Wasu daga cikinsu kuma sun mutu a sanadiyyar rashin lafiya.
KU KARANTA: Ana muzgunawa Kiristocin Najeriya a Yankin Arewa – Okupe
Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai kusan Mata tara da bam ya kashesu a lokacin da su ke tsare. Har gobe akwai fiye da mata 100 da ke hannun Mayakan Boko Haram.
Labaran da ake samu shi ne an yi ta yawo da yaran makarantar daga Chibok zuwa tsaunin Mandara da kuma Gwoza. Wannan wuri ya na makwabtaka da kasar Kamaru.
Wannan yarinya da ta bada labarin cewa ta ga wasu ‘Yan matan na Chibok a Dajin Sambisa ta sake farfado da maganar ceto wadannan Bayin Allah da ke cikin babban hadari.
Sabon bayanin da mu ke ji shi ne wadanda su ka kama wadannan Mata tun farkon 2014, sun fara shiryawa domin su tattauna da gwamnati a kan yadda za su saki yaran.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng