Shin Da Gaske Tchiani Na Nijar Ya Kira Gwamnatin Tinubu Haramtacciya? Bayanai Sun Fito
- Ana ci gaba da dabur-dabur a tsakanin Jamhuriyar Nijar da kungiyar ECOWAS tun bayan hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum daga kan karagar mulki a kasar
- Yayin da ake tsaka da rikicin, wani bidiyo da ya yadu a kafafen sadarwa ya nuna Tchiani na cewa ba zai saurari Tinubu ba don gwamnatinsa haramtacciya ce
- Afrika Check da ta saba binciken irin wadannan al'amura ta yi binciken kwakwaf a kan bidiyon inda ta tabbatar cewa babu kamshin gaskiya a ciki inda Tchiani ya fadi haka
Yamai, Nijar - Wani faifan bidiyo da ya yadu a kafar sadarwa, an gano Janar Abdourahmane Tchiani na Jamhuriyar Nijar na cewa ba zai saurari komai daga haramtacciyar gwamnatin Tinubu ba.
Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin mayar da gwamnatin Mohamed Bazoum kan karagar mulki, Legit.ng ta tattaro.
Wane sako bidiyon ke dauke da shi ga Tinubu?
Tinubu shi ne shugaban Kungiyar Raya Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) inda su ke kiran sojin Nijar da su mika mulki ko su fuskanci karfin soji.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sojin mulkin Nijar sun yi kunnen uwar shegu da dukkan barazanar kungiyar ECOWAS na mika mulki ga Bazoum.
A faifan bidiyon da aka yada a kafar Facebook, Tchiani na cewa:
"Gwamntinka haramtacciya ce, bazan saurare ka ba, Tchiani ya yi wa Tinubu martani a matsayin shugaban ECOWAS."
Binciken kwakwaf kan bidiyon isgili ga Tinubu
Faifan bidiyon na dauke da hoton Tchiani da kuma Shugaba Tinubu inda Tchiani ke magana.
Africa Check ta yi binciken kwakwaf kan zargin da ake kan Tchiani ya ce ba zai saurari Tinubu ba saboda gwamnatinsa haramtacciya ce.
Binciken ya tabbatar da cewa babu inda Tchiani ya fadi haka kuma babu kamshin gaskiya a ciki.
Nijar: Sojin Kasar Sun Yi Fatali Da Barazanar ECOWAS
A wani labarin, shugaban sojin kasar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya yi fatali da barazanar kungiyar ECOWAS ga kasar don mika mulki ga hambararren shugaba Mohamed Bazoum.
ECOWAS ta yi barazanar afkawa Jamhuriyar Nijar idan har ba su mika mulki ga Mohamed Bazoum ba a cikin mako daya.
Kungiyar tun farko ta saka wa kasar Nijar takunkumi da zimmar kuntata musu don mika mulki cikin lalama.
Asali: Legit.ng