Jerin Sanatoci da ‘Yan Majalisa 3 da Su ka Yi Cacar Kujerunsu, Aka Nada su Ministoci Yau
- Bola Ahmed Tinubu ya dauko mutane 45 da su ka zama ministoci bayan watanni biyu a kan mulki
- Majalisar ministocin za ta kunshi ‘yan siyasa, wasunsu sun yi aiki a majalisar wakilai ko dattawa
- David Umahi da Ibrahim Geidam duka Sanatoci ne amma su ka hakura da mukamansu a majalisa
Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da mutanen da za su rike masa ma’aikatun gwamnatin tarayya bayan kusan watanni uku a ofis.
Legit.ng Hausa ta bi jerin sunayen ministocin, ta fahimci akwai wadanda su ke kan mukaman siyasa, amma su ka hakura da kujerunsu.
A majalisar FEC za a samu wadanda sun yi aiki a majalisar wakilai; Nkiruka Onyejeocha, Bello Muhammad Matawalle da Yusuf Sunumu.
Akwai ‘yan siyasan da sun taba zama sanatoci; John Enoh Heineken Lokpobiri, Atiku Bagudu, Sa’idu A. Alkali sai kuma Aliyu Sabi Abdullahi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Amma akwai wadanda kafin a nada su, su na rike da kujeru a majalisar tarayya, su ne:
Ministocin da su ka yi murabus a Majalisa
1. David Umahi
Sanata David Umahi ya sauka daga mukamin Sanatan Ebonyi ta Kudu kuma mataimakin shugaban masu tsawatarwa a majalisa, ya zama ministan ayyuka.
Tsohon gwamnan ya lashe zaben majalisar dattawa ne a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023.
2. Ibrahim Geidam
Sanatan gabashin Yobe ya zama ministan harkokin ‘yan sanda a gwamnati mai-ci. ‘Dan siyasar ya hakura da matsayinsa a majalisa, ya karbi kujera a FEC.
Kamar David Umahi, sabon ministan ya na cikin tsofaffin gwamnonin da Bola Tinubu ya dauko.
3. Bunmi Tunji-Ojo
Hon. Bunmi Tunji Ojo ya yi ban-kwana da majalisar wakilan tarayya da ya amince ya karbi kujerar minista, mutanen yankin Akoko za su samu sabon wakili.
‘Dan siyasar mai shekara 41 a Duniya ya shafe shekaru hudu a majalisa kafin ya nemi tazarce a 2023.
An rantsar da Ministoci
A baya kun ji labari Lateef Fagbemi SAN ya zama babban lauyan gwamnatin tarayyar Najeriya. Babban lauyan ya samu shiga majalisar FEC.
An ratsar da Joseph Utsev da Heineken Lokpobiri tare da sauran ministoci a fadar shugaban kasa a Abuja, watanni biyu bayan nada shugaban kasa.
Asali: Legit.ng