Jerin Ma'aikatu Da Tinubu Ya Yi Sauye-Sauye Da Ministoci Da Ya Nada
- A jiya Lahadi 20 ga watan Agusta, Shugaba Bola Tinubu ya yi sauye-sauye a mukaman ministocin da za a rantsar a yau Litinin 21 ga watan Agusta
- Hadimin Shugaba Tinubu a harkar yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi 20 ga watan Agusta a Abuja
- Shugaba Bola Tinubu ya fara rantsar da sabbin ministocin a yanzu haka a fadar shugaban kasar da ke babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja
FCT, Abuja - Sanarwar sauya ma'aikatun na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a jiya.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shirya rantsar da sabbin ministocin a yau Litinin 21 ga watan Agusta.
Legit.ng ta jero muku sauye-sauyen da kuma ma'aikatunsu.
1. Injiniya Abubakar Momoh
Momoh ya samu sauyi zuwa ma'aikatar ci gaban Neja-Delta bayan sauya masa ma'aikata daga ta matasa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Abubakar Momoh wanda ya fito daga Etsako da ke jihar Edo a baya an nada shi ministan matasa ne.
2. Adegboyega Oyetola
Oyetola ya koma ma'aikatar kula da tattalin arzikin teku.
Tsohon gwamnan na Osun a baya shi ne ministan sufuri kafin sauya masa ma'aikata.
3. Olubunmi Tunji-Ojo
Bunmi ya samu sauyin ma'aikata zuwa ministan harkokin cikin gida
A baya Tunji-Ojo shi ne ministan tattalin arzikin teku a Najeriya.
4. Sanata Sa'idu Alkali
A baya shi ne ministan harkokin cikin gida kafin ya koma ma'aikatar sufuri.
Alkali ya wakilci Gombe ta Arewa a majalisar Dattawa har sau uku.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu yanzu haka ya na rantsar da sabbin ministoci a fadar shugaban kasa da ke babban birnin Tarayya Abuja a yau Litinin 21 ga watan Agusta.
Tibubu Ya Raba Ma'aikatu Ga Sabbin Ministoci
A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya raba mukamai ga sabbin ministoci da ya nada a gwamnatinsa.
Daga cikin ministocin da aka raba wa ma'aikatu akwai tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike da aka ba shi ministan Abuja.
Sai Muhammad Badaru Abubakar da ke rike da ministan tsaro da kuma karamin minsta, Bello Matawalle.
Asali: Legit.ng