Ba Sama Ce Za Ta Fado Ba Idan Kotu Ta Umarci Tsige Tinubu, Inji Jagoran Matasan PDP Kadade
- Shugaban matasan PDP ya caccaki yadda aka ba Tinubu gaskiya a zaben 2023 da aka gudanar a watan Faburairu
- Ya bayyana cewa, ba sama ce za ta fado ba idan aka alanta cewa Tinubu bai lashe zaben 2023 ba a kotun zabe
- An maka INEC, APC da Tinubu a kotu kan zargin yin murdiya a zaben da ya gabata, lamarin da ke kara daukar hankali
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Najeriya - Shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Muhammed Kadade, ya ce ba sammai bane za su fado a kan Najeriya ba idan kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta soke nasarar da Bola Tinubu ya samu.
Ya kara da cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ne halastaccen wanda ya lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Kadade ya bayyana hakan ne a wani sakon bidiyon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ranar Juma'ar da ta gabata.
Atiku Ko Tinubu? Shugaban Matasan PDP Ya Bayyana Wanda Ya Kamata Kotun Zabe Ta Ba Nasara a Zaben 2023
A cewarsa, hukuncin da kotun za ta yanke zai taka muhimmiyar rawa wajen tantance makomar al'ummar kasar nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tinubu dan koyo ne, inji Kadade
Yayin da yake kokawa kan halin kunci da matsin tattalin arzikin da kasar nan ke ciki, jagoran matasan ya ce Tinubu ya tabbatarwa kasa cewa shi dan koyo ne a fannin shugabanci da mulki.
A cewarsa:
“A yau Najeriya ta durkushe a fannin zamantakewa da tattalin arziki. Dole ne mu tashi mu kare mutunci da daukakar da kakanninmu da suka kafa.”
Ya kuma bayyana cewa, yanzu haka ‘yan Najeriya na ci gaba da jiran abin da kotun za ta yanke, kuma akwai yakinin ba Atiku Abubakar gaskiya a nan gaba kadan.
Idan baku manta ba, an yi zaben 2023 a watan Faburairu, inda aka alanta Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe a farkon watan Maris.
Kotu na shirin tsige gwamnan Ebonyi na APC
A wani labarin, kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Ebonyi mai zamanta a Abuja, ta tanadi hukuncinta kan karar da dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP, Ifeanyi Odili da na jam'iyyar APGA, Farfesa Benard Odoh, suka shigar.
Kotun ta tanadi hukuncin na ta ne bayan dukkanin bangarorin sun kammala mika bayanansu, cewar rahoton Channels TV.
Legit.ng ta tattaro cewa ‘yan takarar na PDP da APGA na kalubalantar bayyana ɗan takarar APC, Francis Nwifuru a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan na ranar 18 ga watan Maris 2023.
Asali: Legit.ng