Zaben 2023: Cardinal Onaiyekan Ya Shawarci 'Yan Najeriya Kan Abinda Za Su Yi Idan Kotun Koli Ta Yi Hukunci

Zaben 2023: Cardinal Onaiyekan Ya Shawarci 'Yan Najeriya Kan Abinda Za Su Yi Idan Kotun Koli Ta Yi Hukunci

  • Cardinal John Onaiyekan ya bayyana cewa ƴan Najeriya su shirya amincewa da hukuncin kotun ƙoli kan zaɓen shugaban ƙasa na 2023
  • Malamin addinin ya bayyana hakan ne a wajen taron ƙungiyar Catholic Men karo na 10 a birnin Legas
  • Archdiocese Cardinal Onaiyekan ya yi nuni da cewa hankalin ƴan Najeriya ya koma kan hukuncin da kotun za ta yi a kan zaɓen shugaban ƙasar

Ikoyi, jihar Legas - Babban Bishop na Abuja Cardinal John Onaiyekan, ya bayyana cewa yakamata ƴan Najeriya su amince da hukuncin kotun ƙoli kan zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Malamin addinin ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 19 ga watan Agusta a wajen taron ƙungiyar Catholic Men karo na 10 birnin Legas, wanda aka yi a St Gregory’s College, Ikoyi, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Bi Tsakar Dare Sun Sace Matar Wani Babban Malamin Addini a Jihar Kwara

Onaiyekan ya yi magana kan zaben shari'ar zaben shugaban kasa
Cardinal Onaiyekan ya shawarci 'yan Najeriya kan hukuncin kotun koli Hoto: @realFFK, @ABUSRCJudiciary, @officialABAT
Asali: Twitter

Ido ya koma kan bangaren shari'a, cewar Onaiyekan

Da yake cigaba da bayani, Cardinal Onaiyekan ya bayyana cewa yanzu kowa ya zura ido kan abin da zai faru a kotu. Ya bayyana cewa yakamata ƴan Najeriya su amince da hukuncin da kotun ƙolin za ta yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Shin kotun za ta yanke hukuncin cewa zaɓen ya yi daidai, ko kotun za ta yanke hukunci wanda tun kafin a fara shari'ar mutane da dama sun yanke cewa wannan sakamakon zaɓen ba gaskiya ba ne."
"Abun takaici ne jan ƙafar da kotun ke yi wajen yanke hukuncinta. Amma za mu cigaba da jira har lokacin da kotun za ta yanke hukuncinta."
"Yakamata mu amince da duk hukuncin da kotun ƙoli ta yanke ko ya yi mana daɗi ko akasin hakan. Saboba babu wata kotun bayan kotun ƙoli. Za mu bar komai a hannun ubangiji."

Kara karanta wannan

Tinubu vs Atiku, Obi: An Gargadi Kotun Zaben Shugaban Kasa Kan Yin Hukuncin Da Zai Haifar Da Rikici a Kasa

Wanda Yakamata Kotu Ta Ba Nasara

A wani labarin na daban kuma, shugaban matasan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bayyana wanda yakamata kotun ƙoli ta ba nasara a ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu da ake yi a gabanta.

Muhammad Kadade shugaban matasan na jam'iyyar ta PDP, ya buƙaci kotun ƙolin da ta ayyana ɗan takarar jam'iyyar, Alhaji Atiku Abubakar, a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasar na 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng