Matashi Ya Mayar Da Kansa Kare Da $14,000, Har Ya Fito Bainar Jama'a? Gaskiya Ta Bayyana

Matashi Ya Mayar Da Kansa Kare Da $14,000, Har Ya Fito Bainar Jama'a? Gaskiya Ta Bayyana

  • Karin bayani ya fito game da bidiyo da hotunan mutumin da aka yi ikirarin cewa ya sauya halittarsa zuwa kare
  • Binciken kwakwaf ya nuna an yi lamarin bahaguwar fassara ne domin dai riga ce aka dinka na kare
  • Wani mai amfani da Facebook da ya nuna rashin gamsuwa da lamarin ya ce babu fasaha ko wani wanda zai iya mayar da mutrum dabba

Wani mai amfani da Facebook, EmmyG, ya yi ikirarin cewa labarin wani mutum da ya mayar da kansa kare da $14,000 sannan ya fito bainar jama'a a karo na farko duk soki burutsu ce.

Bidiyon mai tsawon sakanni 44 ya nuno wata mata da ba a bayyana sunanta ba tsaye a gefen karen yayin da matafiya a kafa ke ta giftawa.

Matashi ya karyata labarin mutumin da ya mayar da kansa kare
Matashi Ya Mayar Da Kansa Kare Da $14,000? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: I want to be an animal
Source: Youtube

A daidai lokacin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya tara fiye da mutum miliyan 13 da suka kalla, sannan yana da 'likes' fiye da dubu 19 da martani sama da miliyan 4.9.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Elon Musk zai kawo wani sabon tsarin da ba a taba ba a Twitter

Yayin da tsarin sauya halitta ya zama ruwan dare a duniya, ikirarin cewa mutum yana iya mayar da kansa zuwa wani dabba ya zama babban lamari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wani mai amfani da Facebook, Dycen Victor, ya nuna rashin yadda da rubutun sannan ya yanke shawarar cewa riga ce aka dinka. Ya ce:

"Wannan ba gaskiya ba ne; babu fasaha ko wani wanda zai iya yin wannan. Riga ce."

Sai dai kuma, wani yunkuri da Legitng ta yi ya nuna cewa kawai an yi wa bayani mai muhimmanci bahaguwar fassara ne.

Kuskure na farko game da wani mutum da ake zargin ya koma kare

Wani bincike da aka yi a tsanaki kan bidiyon ya nuna cewa an nuna wasu halaye na karnuka a cikin hoto da bidiyon da ya yadu. Misali, ya dingisa yayin da yake kwance a kasa maimakon tafiya a mike.

Haka kuma, wannan din bai motsa fuska ko bude bakinsa ba, hatta ga lokacin da ya yi birgima a kasa lokacin da matar da ke rike da shi ta yi.

Kara karanta wannan

Arziki nufin Allah ne: Mutumin da ya zauna a Kanada tsawon shekaru 20, ya dawo ba nauyi

Mutumin kasar Japan da ya kashe makudan kudi wajen siyan rigar kare

Mun dai ji labarin wani mutumin kasar Japan, mai suna Toco ya yi suna sosai a yanar gizo bayan fitowarsa a karon farko a matsayin mutumin kare.

Toco, wanda ya samu tarin mabiya a YouTube da TikTok, ya biya wani kamfani mai suna Zeppet zunzurutun kudi har naira miliyan 10.7 domin dinka masa kayan kare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng