Munashe Ncube: Matar aure da take zina da maza 16 a titi

Munashe Ncube: Matar aure da take zina da maza 16 a titi

- Wata mata mai suna Munashe Ncube ta gudu inda ta bar gidanta bayan asirinta ya tonu na mu'amala da maza 16

- Mijinta ya koka da yadda sauran samarinta kan kira shi tare da zaginshi saboda matar shi da suke soyayya da ita

- Makomo ya tsinkayi hirar matar shi da samarinta 16 tare da bidiyon yadda suke lalata da matar shi amma ba ta yadda da shi

Wata matar aure ta bar gidanta a kunyace bayan da asirinta na mu'amala da wasu maza 16 ya tonu.

Munashe Charlene Ncube mai shekaru 24 ta Damofalls an zargeta da kwanciya da mazan 16 har da mijinta na 17. Tayi kwanaki uku tare da wani saurayi yayin hutun bikin Kirsimeti.

Ncube ta gudu bayan da mijinta mai suna Erkridice Makomo ya gano hirarta, bidiyo da kuma hotunanta tare da samarin nata, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Munashe Ncube: Matar aure da take zina da maza 16 a titi
Munashe Ncube: Matar aure da take zina da maza 16 a titi
Asali: Facebook

Makomo ya matukar fusata daga yadda hirar matar shi ta kasance da samarinta. Ya koka da yadda matar tashi take hana shi hakkin shi. Ta kan yi mishi koke a kan ciwon ciki amma sai taje tana ba wasu mazan waje.

Makomo ya ce wasu samarin nata na kiran shi tare da zaginshi. Aurensu yayi shekaru hudu.

KU KARANTA: Tashin hankali: Mutanen gari sun bugu sunyi mankas, bayan 'yan sanda sun kone mota guda ta tabar wiwi

"Na sha matukar mamaki a rayuwata bayan na ga hirar matata da samarinta 16 wanda ta boye a manhajar WhatsApp. Na gano cewa a watan Disamba da ta gabata ta je tayi kwanaki uku da wani saurayinta mai suna Kudakwashe Masoka yayin Kirsimeti. Bata son bani hakkina amma tana ba wasu a waje."

Makomo ya ce Ncube ta sace mishi dala 40 kuma yana zaton wajen Kudakwashe ta koma.

Daya bayan daya aka dinga zakulo samarinta kuma an hada musu kungiya a manhajar WhatsApp wacce suke bayyana hira da hotunansu tare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel