Jerin Ministocin Tinubu 5 Da Za Su Kula Da Harkokin Tsaro A Najeriya
Babu bangaren da 'yan Najeriya su ka fi bukatar sauyi cikin gaggawa kamar harkar tsaro, ganin yadda bangaren ke lakume makudan kudade a kasar musamman lokacin kasafin kudi na karshen shekara
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Rashin tsaro ta dawo babbar barazana ga kasancewar Najeriya inda ya mamaye kasar baki daya daga Arewaci har zuwa Kudanci.
A kokarin dakile matsalar tsaro, Shugaba Bola Tinubu ya daura nauyin kawo karshen rashin tsaron ga ministoci biyar.
Kamar yadda @Statisense ya wallafa, wadannan su ne jerin ministoci da ke da alhakin kawo karshen rashin tsaron.
1. Ministan Tsaro - Mohammed Badaru Abubakar
Badaru wanda tsohon gwamnan jihar Jigawa ne ya kasance shi ne babban ministan tsaro.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Zai samu taimako daga karamin minista a ma'aikatar, Bello Matawalle na jihar Zamfara.
2. Karamin Ministan Tsaro - Bello Matawalle
Matawalle, tsohon gwamnan jihar Zamfara, zai yi aiki tare da Badaru a ma'aikata daya a matsayin karamin minista.
3. Ministan Harkokin Cikin Gida - Sanata Sa'idu Alkali
Alkali shi zai jagoranci ma'aikatar cikin gida da ta ka kunshi hukumomin shige da fice da fasa kwauri da kuma hukumar kashe gobara da sauransu.
4. Ministan Harkokin 'Yan Sanda - Ibrahim Geidam
Sanata Geidam shi ne tsohon gwamnan jihar Yobe kuma Sanata da ya ke wakiltar Yobe ta Gabas.
Geidam ya taba yin mataimakin gwamnan jihar Yobe kafin daga bisani ya samu nasarar kasancewa gwamnan jihar a jam'iyyar APC.
5. Karamar Ministar Harkokin 'Yan Sanda - Imaan Sulaiman
Imaan ita ce tsohuwar babbar daraktar hukumar yaki da safarar mutane (NAPTIP).
Matashiyar ta fito daga jihar Nasarawa inda ta ke kokarin kammala karatunta na digirin digirgir.
Matsalolin tsaro a Najeriya
Najeriya na fama da matsalolin tsaro tun da dadewa da su ka hada da ta'addanci da masu garkuwa da kuma fashi da makami, Legit.ng ta tattaro.
Rashin tsaron ya ratsa kasar baki daya daga Kudanci har Arewacin Najeriya da ya kasance ruwan dare.
Tinubu Ya Raba Mukaman Ministoci 45 Da Aka Tantance
A wani labarin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya raba mukaman ministoci 45 da aka kammala tantancewa a majalisar Dattawa a kwanakin baya.
Daga cikin wadanda ba su samu tabbatarwa daga majalisar ba akwai Nasiru El-Rufai daga jihar Kaduna da Sanata Sani Danladi daga Taraba sai kuma Stella Oketete daga jihar Delta.
Asali: Legit.ng