Tinubu: Za a Saida NNPC da Wasu Kamfanonin Gwamnati Rututu Domin a Samu Kudi

Tinubu: Za a Saida NNPC da Wasu Kamfanonin Gwamnati Rututu Domin a Samu Kudi

  • Gwamnatin tarayya za ta iya yin gwanjon wasu daga cikin manya-manyan kamfanonin da ta mallaka
  • Za ayi hakan ne da nufin Najeriya ta samu kudin shiga, kuma a ci moriyar kadarorin yadda ya kamata
  • Tun ba yau, jagoran adawa, Atiku Abubakar ya na da ra’ayin a cefanar da irinsu kamfanin NNPC, a huta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Gwamnatin Najeriya ta fara tunanin saida kasonta da ke cikin kamfanoni kusan 20, za ayi hakan ne saboda a samu kudin shiga.

A ranar Talata, rahoto ya fito daga Bloomberg cewa NNPC ya na cikin kamfanonin da gwamnatin tarayya ta ke tunanin saida hannun jarinta.

Shugaban kamfanin MOFI, Armstrong Takang ya bayyana wannan shirin da gwamnati ta ke yi. MOFI ke kula da kadarorin gwamnati.

Bola Tinubu
Bola Tinubu zai saida hannun jarin NNPC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Cefanar da kayan gwamnati

Da aka zanta da shi ta wayar salula, Takang ya fadawa jaridar kasar wajen cewa su na tunanin yin gwajon wasu kayan gwamnati a kasuwa.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Karin Bayani a Kan Yiwuwar Dawo da Tallafin Man Fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na kamfanin MOFI yake cewa za su aiwatar da wannan shiri ne a cikin watanni 18, 'yan kwanaki kadan bayan cire tallafin fetur.

An samu N1tr a shekaru 32

Kafin yanzu, This Day ta ce gwamnatin tarayya ta karkashin hukumar BPE, ta samu Naira tiriliyan 1 daga gwanjon kayan gwamnati da aka yi

Alex Okoh ya ce a tsawon shekaru 32, an yi gwanjon kadarori da dukiyoyi 234 da gwamnati ta mallaka, hakan ya sa an samu kudin shiga.

A shekarar 1989 ana amfani da kwamitin TCPC ne, sai a 1999 aka kafa hukumar nan ta BPE, Malam Nasir El-Rufai ne ya fito da sunanta sosai.

Manufar gwamnatin Tinubu

Gwamnatin tarayya ta nuna abin da ta ke so a shi ne jama'a su iya amfana sosai da kadarorin, ba kurum ya zama Najeriya ta na da iko ba.

Kara karanta wannan

Uwar Bari ta Jawo Shugaba Tinubu Ya Fara Shirin Dawo da Tallafin Man Fetur

"Wasu daga cikin kamfanonin su na bukatar ‘yan kasuwa su samu mafi yawan hannun jarin, amfani ake bukata ba iko da su ba.
Zai fi kyau mu mallaki 49% na hannun jari a kamfanin da yake aiki a maimakon mu mallaki 90% a kamfanin da bai aiki da kyau.

- Armstrong Takang

Tarihin aikin MOFI a kasar nan

Tun a shekarar 1959, MOFI ya ke aiki a Najeriya domin kula da muhimman kadarorin da ake da su a bangaren sufuri, mai, kudi da kuma masana’antu.

Muhammadu Buhari ya dauko Wale Edun, ya ba shi shugabancin hukumar. A yanzu Edun ya na cikin masu ba Bola Tinubu shawara a harkar kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng