Putin Ya Bukaci a Sasanta Rikicin Nijar Cikin Lumana, Ya Gana Da Shugaban Mulkin Sojan Mali

Putin Ya Bukaci a Sasanta Rikicin Nijar Cikin Lumana, Ya Gana Da Shugaban Mulkin Sojan Mali

  • Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin, ya tofa albarkacin bakinsa kan rikicin jamhuriyar Nijar
  • Shugaba Putin ya buƙaci a bi matakai na diflomasiyya wajen sasanta rikicin na Nijar
  • Ya bayyana hakan ne, a yayin da yake zantawa da shugaban ƙasar Mali na mulkin soji Assimi Goita

Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya yi kira da a bi matakai na lumana wajen sasanta rikicin jamhuriyar Nijar.

Ya yi wannan kira ne a yayin da yake tattaunawa da shugaban ƙasar Mali na mulkin soji Assimi Goita, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Shugaban ƙasar Rasha ya tofa albarkacin bakinsa kan rikicin Nijar
Putin ya buƙaci a warware rikicin Nijar cikin lumana. Hoto: PressExpress Nigeria
Asali: Facebook

Putin ya gana da shugabannin juyin mulkin ƙasashen Afrika ta Yamma

Tun bayan hamɓarar da gwamnatin Mohamed Bazoum na Nijar da sojoji suka yi, Shugaba Putin ya gana da wasu daga cikin shugabannin sauran ƙasashen na mulkin soji.

Kara karanta wannan

Abinda Sakataren Amurka Ya Faɗawa Tinubu Kan ECOWAS Dangane Da Juyin Mulkin Nijar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ko a makon da ya gabata, Putin ya gana da shugaban rikon kwarya na Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore kan rikicin na jamhuriyar Nijar.

An yaɗa jita-jitar cewa wannan zaman na daga cikin shirye-shiryen da Putin yake yi na zama da duka shugabannin ƙasashen Afrika ta Yamma na mulkin soji.

Kasar Mali dai ta ƙulla alaƙa da Rasha ne tun a shekarar 2020 lokacin da sojoji suka kifar da gwamnati mai ci kamar yadda France 24 ta wallafa.

Sakataren Amurka Anthony Blinken ya kira Shugaba Tinubu a waya

Wani labari da Legit.ng ta yi a baya, ya nuna cewa sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken, ya kira Shugaba Bola Tinubu a wayar tarho.

Blinken ya kira Tinubu ne domin ya jinjina ma sa kan irin yadda yake tafiyar da shugabancin kungiyar ECOWAS.

Kara karanta wannan

Firaministan Nijar Ya Fadi Abinda Za Su Yi Dangane Da Takunkumin Da ECOWAS Ta Sanya Mu Su

Ya ce Tinubu na ƙoƙari sosai wajen tafiyar da ECOWAS, musamman ma wajen ƙoƙarin ganin an dawo da mulkin dimokuradiyya a jamhuriyar Nijar.

ECOWAS ta gargaɗi sojojin Wagner na Rasha kan shiga rikicin Nijar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan gargaɗin da ƙungiyar ECOWAS ta yi wa dakarun haya na ƙasar Rasha wato Wagner.

Ta gargaɗe su kan yin katsalandan a cikin rikicin jamhuriyar Nijar, inda ta bayyana cewa za ta ɗora alhakin duk abinda suka yi a kan ƙasar Rasha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng