Sakataren Amurka Antony Blinken Ya Kira Tinubu Kan Shugabancin ECOWAS, Cikakkun Bayanai Sun Fito

Sakataren Amurka Antony Blinken Ya Kira Tinubu Kan Shugabancin ECOWAS, Cikakkun Bayanai Sun Fito

  • An jinjinawa Shugaba Tinubu bisa salon yadda yake tafiyar da ECOWAS, musamman a kan rikicin Nijar
  • Sakataren Amurka Anthony Blinken ya ce ya kira Shugaba Tinubu kuma ya jinjina masa kan ƙoƙarin dawo da dimokuraɗiyya a Nijar
  • Hakan na zuwa ne a lokacin da sojojin na Nijar suka amince su tattauna da ƙungiyar ECOWAS don samar da masalaha

Fadar White House, Amurka - Sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken, ya jinjinawa Shugaba Bola Tinubu kan salon shugabancinsa a kungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS).

Blinken ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X wanda a da ake kira Twitter, a ranar Litinin 14 ga watan Agusta.

Ya ce ya kira Shugaba Tinubu inda ya jinjina ma sa kan salon shuagabancin na sa a ECOWAS.

Kara karanta wannan

Firaministan Nijar Ya Fadi Abinda Za Su Yi Dangane Da Takunkumin Da ECOWAS Ta Sanya Mu Su

Blinken ya kira Shugaba Tinubu a waya
Sakataren Amurka ya jinjinawa Tinubu kan shugabancin ECOWAS. Hoto: @SecBlinken, @OfficialABAT
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matakan da ECOWAS ta ɗauka kan sojojin Nijar

Tun bayan sanar da hamɓarar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum da sojojin Nijar suka yi, ECOWAS ta ɗauki tsauraran matakai a kan sojojin da suka yi juyin mulkin.

ECOWAS ƙarƙashin shugabancin Shugaba Bola Tinubu, ta bai wa sojojin wa'adin kwanaki bakwai su mayar da mulki ko su fuskanci mataki mai tsauri, ciki kuwa har da amfani da ƙarfin soji.

ECOWAS ta kuma ɗauki ƙarin wasu tsauraran mataka ciki har da datse wutar lantarkin da Najeriya take bai wa jamhuriyar Nijar.

Abinda ECOWAS ke yi don ganin ta kawar da mulkin sojojin Nijar

A ci gaba da ganin ta kawo ƙarshen mulkin sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar, ECOWAS ta ɗauki ƙarin matakai da suka haɗa da amshe kadarori da riƙe kuɗaɗen wasu da ke da hannu a juyin mulkin.

Kara karanta wannan

Amurka Ta Yi Gargaɗi Mai Zafi Ga Sojojin Nijar Kan Taba Lafiyar Bazoum Da Ta Iyalansa

Sai dai kuma amfani da ƙarfin soji da ECOWAS ta yi iƙirarin yi ya janyo fargaba, musamman ma da ake ganin sojojin haya na Wagner, waɗanda mallakin Rasha ne na goyawa sojojin Nijar baya.

Sai dai ana cikin wannan yanayi na fargabar ne aka jiyo sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken na yabawa salon shugabancin Tinubu a ECOWAS.

Tchiani zai tattauna da ECOWAS

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan amincewar da shugaban juyin mulkin jamhuriyar Nijar, Abdourahmane Tchiani ya yi na tattaunawa da ƙungiyar ECOWAS.

Sabon Firaministan Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine ne ya bayyana hakan, inda ya ce za a yi tattauanawar nan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel